Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

NASARAWA: ‎Al'ummar Akwanga Sun Yaba Da Ƙoƙarin Tinubu Na Gina Katafaren Asibitin ƙwararru Da Gadojin Sama

   ‎Al’ummar garin Akwanga da ke Jihar Nasarawa sun bayyana jin daɗinsu tare da yabawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan aikin gini da faɗ...

  
‎Al’ummar garin Akwanga da ke Jihar Nasarawa sun bayyana jin daɗinsu tare da yabawa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan aikin gini da faɗaɗa katafaren Asibitin Kwararru na Akwanga.

‎Al’ummar sun bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da wakilan kafafen yaɗa labarai suka yi da su, inda suka ce aikin asibitin na daga cikin muhimman ayyukan da za su taimaka wajen inganta harkar kiwon lafiya a yankin da ma Najeriya baki ɗaya.

‎A cewar mazauna yankin, ginin wannan katafaren asibiti zai taimaka wajen rage wahalar da al’umma ke fuskanta wajen neman kulawar lafiya, musamman marasa lafiya da ke bukatar kulawar kwararrun likitoci da kuma wasu nau’o’in magani na musamman.

‎Asibitin Akwanga, wanda a baya yake matsayin General Hospital, yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ɗaga darajarsa zuwa Asibitin Kwararru (Specialist Hospital), tare da samar da ƙarin kayayyakin aiki da gine-ginen da suka dace da sabon matsayinsa.

‎Wannan mataki na daga cikin kokarin ƙarfafa tsarin kiwon lafiya a matakin tarayya, tare da samar da cibiyoyin lafiya masu inganci da za su iya kula da marasa lafiya daga Akwanga da sauran ƙananan hukumomi da garuruwan da ke kewaye da yankin.

‎AIKIN YA YI NISA

‎A yayin ziyarar gani da ido, wakilan kafafen yaɗa labarai sun ga yadda aikin ginin asibitin ya samu babban ci gaba, inda ake ci gaba da gudanar da ayyuka daban-daban a harabar asibitin.

‎Al’umma sun ce ci gaban aikin ya nuna cewa gwamnati na ɗaukar batun kiwon lafiya da muhimmanci, tare da fatan ganin an kammala aikin cikin lokaci domin jama’a su fara amfana da shi.

‎Sun kuma bayyana godiya ga Shugaba Tinubu kan kulawar da yake bai wa ayyukan ci gaba a Jihar Nasarawa, musamman waɗanda suka shafi kiwon lafiya.

‎Wannan aiki na Asibitin Kwararru na Akwanga na ƙarƙashin manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙara inganta abubuwan more rayuwa da kuma samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga ‘yan Najeriya.

‎Ayyukan gwamnati na samun ƙarin kulawa da yaɗa bayanai daga ɓangaren kafafen yaɗa labarai na fadar shugaban ƙasa, ƙarƙashin jagorancin mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, da babban hadimin Shugaban Ƙasa kan harkokin kafafen yaɗa labarai, Abdulaziz Abdulaziz.

‎Al’ummar Akwanga sun ce suna fatan aikin zai kammala cikin nasara, domin asibitin ya fara bayar da cikakkiyar hidimar kiwon lafiya ga al’ummar yankin da sauran ‘yan Nijeriya.








 

No comments