Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BATANCI GA SHAIKH ƊAHIRU BAUCHI: Baffa Hotoro Ya Ƙi Bayyana Gaban Kotu, An Sake Sanya Rana A Karo Na Uku

Shari’ar da ake yi wa wani mai iƙirarin malamta a Kano, Adam Zubair Adam, wanda aka fi sani da Baffa Hotoro, kan zargin aikata laifukan inta...


Shari’ar da ake yi wa wani mai iƙirarin malamta a Kano, Adam Zubair Adam, wanda aka fi sani da Baffa Hotoro, kan zargin aikata laifukan intanet da kuma ɓata sunan marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da Sheikh Munir Adam Koza, ta sake fuskantar tsaiko bayan wanda ake ƙarar ya ƙi halartar zaman kotu.

Shari’ar da ke gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsaya cak ne a karo na uku sakamakon rashin halartar Baffa Hotoro, wanda ake tuhuma da yin kalaman batanci da ɓata suna ga malaman addinin biyu, wanda hakan na iya zama barazana ga zaman lafiyar al'umma.

Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a M.S. Liman, ta ɗage shari’ar zuwa 19 ga Oktoba, 2026, domin sake yi wa malamin sammaci da fara gabatar da shi a gaban kotu.

Baffa Hotoro na fuskantar tuhume-tuhume guda biyu a ƙarƙashin Dokar Laifukan Intanet ta 2015, wadda aka yi wa kwaskwarima a 2024 (Cybercrime Act), a ƙarƙashin shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CR/87/2026.

Kotun ta taɓa sanya ranakun 23 ga Afrilu, 21 ga Mayu da 22 ga Yuli, 2026 domin ci gaba da shari’ar, amma rashin halartar wanda ake tuhuma ya haifar da dage zaman.

Jami'an 'yan sanda sun kama Baffa Hotoro a watan Fabrairun 2026, daga bisani aka ba da shi beli. An shirya fara gabatar da shi a gaban kotu ranar 23 ga Afrilu, amma bai bayyana ba, lamarin da ya sa kotun ta ɗage shari’ar zuwa 21 ga Mayu.

Lokacin da shari’ar ta sake zuwa gaban kotu a ranar 21 ga Mayu, wanda ake tuhuma bai halarta ba, kuma bai aiko da wani lauya da zai wakilce shi ba. Daga nan aka sake ɗage shari’ar zuwa 22 ga Yuli.

A zaman da ya gabata, Baffa Hotoro bai bayyana a kotu ba, sai dai wani lauya mai suna Amos, wanda ya bayyana a matsayin wakilinsa, ya gabatar da takardar likita da ke nuna cewa malamin ba shi da lafiya kuma ba zai iya zuwa kotu ba.

Sai dai an lura cewa a daidai lokacin da ake gudanar da shari’ar, rahotanni sun nuna cewa malamin yana harkokin sa a kafafen sada zumunta, inda aka gan shi a wani shirin Facebook na kai-tsaye (livestream).

Bisa la’akari da yanayin da ake ciki, ’yan sanda sun yi ƙoƙarin tabbatar da halartar wanda ake tuhuma, ciki har da ƙoƙarin kama shi, amma ba su yi nasara ba.

Daga bisani kotun ta sake ɗage shari’ar zuwa 19 ga Oktoba, 2026, domin gabatar da Sheikh Hotoro a gaban kotu.

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Nijeriya (IGP) ne mai ƙarar, yayin da Baffa Hotoro yake matsayin wanda ake ƙara.

No comments