Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Alummar Jihar Nasarawa Su Yi Murna Da Ayyukan Shugaba Tinubu Na Raya Kasa ‎

*‎Tinubu na shirin Sauya tsarin arewa daga Duhu zuwa Haske.  ‎  ‎ A yayin da ake ci gaba da bayyana ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Shugaba B...


*‎Tinubu na shirin Sauya tsarin arewa daga Duhu zuwa Haske. 
‎ 
‎ A yayin da ake ci gaba da bayyana ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa a sassan Nijeriya, wasu wakilan kafafen yaɗa labarai sun isa Jihar Nasarawa domin ganin ayyukan da idonsu, tare da tantance yadda suke tasiri ga rayuwar al’umma.

‎Ziyarar ta bai wa wakilan kafafen yaɗa labaran damar zagayawa wasu muhimman wurare da ake aiwatar da manyan ayyukan more rayuwa, da wakilan Fadar Shugaban kasa, Karkashin Hadimin Shugaba Tinubu, Bayo Onanuga, da Hadimin Shugaba Tinubu a bangaren kafafen yada labarai, Abdulaziz-abdulaziz, da Dada Olusegun, da sauran tawagar su.

‎An ziyarci  masana’antun  bunƙasa sana’o’in hannu a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Nasarawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna  jihar, Injiniya Abdullahi A. Sule.

‎Manyan ayyukan more rayuwa:
‎Daga cikin wuraren da tawagar ta ziyarta akwai katafariyar Sakatariyar Gwamnatin Jihar Nasarawa, wadda ke daga cikin manyan gine-ginen dgwamnati da ake amfani da su wajen inganta ayyukan gudanar da mulki da samar da yanayi mai kyau ga ma’aikatan gwamnati da al’umma.

‎Haka kuma, tawagar ta duba wasu manyan hanyoyi, ciki har da hanyar Shabu, wadda ke da muhimmiyar alaƙa da zirga-zirgar jama’a da harkokin kasuwanci zuwa wasu sassan jihar da kuma hanyar Taraba.

‎Wadannan ayyuka, a cewar mazauna yankin, suna taimakawa wajen rage wahalhalun sufuri tare da buɗe ƙofofin kasuwanci da zuba jari.

‎Wata muhimmiyar cibiyar da tawagar ta ziyarta ita ce wuraren koyar da walda da sauran sana’o’in hannu, waɗanda aka samar domin bai wa matasa damar samun sana’a da dogaro da kansu.

An bayyana cewa irin waɗannan shirye-shirye na da matuƙar muhimmanci wajen rage zaman kashe wando da kuma bai wa matasa damar zama masu amfani ga kansu, iyalansu da al’umma.

Shugaba Tinubu, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Jihar Nasarawa, na ƙoƙarin ganin an ƙara saka jari a fannin ƙarfafa matasa da samar da hanyoyin dogaro da kai.

Tawagar ta kuma kai ziyara wasu yankunan da ambaliyar ruwa ta taɓa, inda aka gudanar da ayyukan gyaran manyan kwalbatin ruwa da magudanan ruwa domin rage barazanar ambaliya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Daga cikin wuraren da aka duba akwai yankin Hanyar Lafiya zuwa Doma, da kuma Gadar Kilema a cikin birnin Lafiya, inda ake ganin ayyukan gyaran ababen more rayuwa sun taimaka wajen inganta zirga-zirga da sauƙaƙa rayuwar mazauna yankin.

‎Mazauna yankunan da tawagar ta ziyarta sun bayyana farin cikinsu kan ayyukan da ake gudanarwa, inda suka ce inganta hanyoyi, magudanan ruwa, samar da sana’o’i da sauran ayyukan more rayuwa na taimakawa wajen sauƙaƙa rayuwarsu.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce suna fatan ayyukan za su ci gaba da yaɗuwa zuwa sauran sassan jihar domin ƙarin jama’a su amfana.
‎Arewa na fuskantar sabon salo na ci gaba?

Abin da tawagar ta gani a yayin ziyarar ya nuna cewa wasu yankunan Arewa na samun ƙarin ayyukan more rayuwa da shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki.

Masu goyon bayan gwamnatin Shugaba Tinubu na kallon waɗannan ayyuka a matsayin wani ɓangare na shirin sabunta abubuwan more rayuwa da ƙarfafa tattalin arzikin yankunan Arewa, yayin da suke bayyana burin ganin Arewa ta samu ci gaba mai ɗorewa har ta kai matsayin manyan biranen duniya.

A Nasarawa, abin da ya fi bayyana shi ne yadda haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar ke ƙoƙarin mayar da wasu muhimman ayyukan raya ƙasa zuwa abubuwan da jama’a za su iya gani da idonsu.











 

No comments