Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC ƙarƙashin tsarin Kwankwasiyya, tsohon mataimakin gwam...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NDC ƙarƙashin tsarin Kwankwasiyya, tsohon mataimakin gwamna Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a matsayin mutum mai gaskiya, riƙon amana da mutunta al’umma.
Hon. Yusuf Hassan Darma ne ya bayyana hakan tare da tabbatar da cewa irin waɗannan halaye ne suka sa al’umma ke nuna cikakkiyar gamsuwa da cancantar ba shi takara da aka yi.
Ya ƙara da cewa rikon amanar Kwamared Aminu Abdussalam ne ya sa bai taɓa saba layi a tafiyar jagoransu na Kwankwasiyya, Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ba.
Ya yi nuni da cewa: “Kwamared Aminu Abdussalam ɗan siyasa ne gogagge da ya fara siyasa tun daga tushe. Mutane suna aminta da tafiyarsa saboda yana tare da jama’a a kowane yanayi” inji Darma.
Hon. Yusuf Hassan Darma, wanda ke daga cikin makusantan siyasar Kwamared Aminu Abdussalam, ya bayyana shi a matsayin mutum mai faɗa da cikawa, tsayawa kan gaskiya da adalci, kuma mai son cigaban al’umma.
A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su ba wa ‘yan takarar jam’iyyar NDC cikakken haɗin kai da goyon baya a dukkan matakin zabe domin samun nasara.
Hon. Yusuf Hassan Darma ya ce yana da yakinin Kwamared Aminu Abdussalam zai kawo sauyi mai nagarta wajen magance matsalolin da gwamnatin yanzu ta yi watsi da su idan ya zama Gwamnan Kano a zaben 2027.da yardar Allah.

No comments