Yaƙin da ke tsakanin Amurka da Iran ya sake ɗaukar sabon salo bayan da Amurka ta sanar da kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Iran a ƙarshe...
Yaƙin da ke tsakanin Amurka da Iran ya sake ɗaukar sabon salo bayan da Amurka ta sanar da kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Iran a ƙarshen mako, yayin da rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran ta ce ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan wani sansanin sojojin Amurka.
Rahotanni sun bayyana cewa hare-haren na baya-bayan nan sun kasance wani sabon babi na musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu duk da ci gaba da tattaunawar neman kawo ƙarshen yaƙin da ya shafe kusan watanni uku yana ci gaba.
A wata sanarwa da Rundunar Tsakiyar Sojojin Amurka (CENTCOM) ta wallafa, ta ce hare-haren da ta kai a gabar tekun Fasha ta Iran sun biyo bayan abin da ta kira “ayyukan ta’addanci da tsokana” daga Iran, ciki har da harbo jirgin leƙen asirin Amurka mara matuƙi kirar MQ-1 da ke shawagi a sararin samaniyar ƙasa da ƙasa.
Sanarwar ta ce jiragen yaƙin Amurka sun yi gaggawar mayar da martani ta hanyar lalata wasu tsarin kariyar sararin samaniyar Iran, cibiyar kula da hare-hare daga ƙasa da kuma wasu jiragen yaƙi marasa matuƙi guda biyu da ake zargin suna barazana ga jiragen ruwa da ke zirga-zirga a yankin.
Amurka ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da kare muradunta da kadarorinta yayin da yarjejeniyar tsagaita wuta ke ci gaba da aiki.
A nata ɓangaren, Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta kai hari kan wani sansanin jiragen saman da Amurka ke amfani da shi wajen kai hare-hare a kudancin Iran, sai dai ba ta bayyana sunan sansanin ba.
A halin da ake ciki kuma, rahotanni daga ƙasar Kuwait sun nuna cewa tsarin kariyar sararin samaniyar ƙasar ya yi nasarar kakkabo wasu makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi bayan da aka ji karar ƙararrawar gaggawa a sassa daban-daban na ƙasar.
Kamfanin Dillancin Labaran Ƙasar Kuwait (KUNA) ya ruwaito cewa an fuskanci hare-haren ne a yankunan da ke kusa da sansanonin sojin Amurka, amma bai bayar da cikakken bayani kan asarar da aka yi ba.
Tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a farkon watan Afrilu, Amurka da Iran na ci gaba da musayar hare-hare lokaci zuwa lokaci, lamarin da ke nuna yadda tattaunawar neman cimma yarjejeniya mai ɗorewa ke fuskantar cikas.
Yaƙin da Amurka da Isra’ila suka fara a ranar 28 ga Fabrairu ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, musamman a Iran da Lebanon. Haka kuma ya haifar da matsin tattalin arziki a duniya sakamakon tashin farashin makamashi bayan Iran ta takaita zirga-zirga ta Mashigin Hormuz, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai a duniya.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa babban manufarsa ita ce hana Iran mallakar makamin nukiliya, yana mai cewa ƙasar na da wadataccen sinadarin uranium da aka sarrafa sosai. Sai dai gwamnatin Tehran ta ci gaba da musanta zargin cewa tana neman ƙera makaman nukiliya.
A gefe guda, Trump na fuskantar matsin lamba daga cikin gida domin a sake buɗe Mashigin Hormuz domin rage farashin man fetur a Amurka kafin zaɓukan ‘yan majalisa na watan Nuwamba. Haka kuma yana fuskantar suka daga masu tsattsauran ra’ayi a jam’iyyarsa kan yiwuwar sassauta matsin lamba ga Iran.
Har yanzu dai ɓangarorin biyu na ci gaba da saɓani kan muhimman batutuwa, ciki har da buƙatar Iran na a ɗage mata takunkuman tattalin arziki da kuma sakin biliyoyin dalolin kuɗaɗen man fetur nata da aka daskarar a bankunan ƙasashen waje.

No comments