Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jigo a tsarin Kwankwasiyya a Jihar Kano daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Ambasada Isyaku Yahaya Talba, ya bayyana ...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Jigo a tsarin Kwankwasiyya a Jihar Kano daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, Ambasada Isyaku Yahaya Talba, ya bayyana zaÉ“in da jam’iyyar NDC Æ™arÆ™ashin jagorancin Kwankwasiyya ta yi na tsayar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin É—an takarar Gwamna, da cewa zaÉ“i ne da aka yi bisa cancanta.
Ambasada Isyaku ya bayyana hakan ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Kano cikin makon nan.
Ya ce, kamar yadda jagoran su na siyasa, wato Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ya tabbatar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo mutum ne mai riƙo da gaskiya, amana, da ilimin addini. Ya ƙara da cewa mutanen da suka san shi suna da kyakkyawar shaida a kan sa kuma za su ba shi goyon baya don ya kai ga nasara.
Amb. Talba ya kuma nuna gamsuwar sa da tsayar da Dakta Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar a matsayin É—an takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, tare da dukkanin ‘yan takarar jam’iyyar a kowane mataki a Jihar Kano.
Ya bayyana cewa suna bin tsarin Kwankwasiyya ne saboda gamsuwa da akidar kishin al’umma, gina Æ™asa da son cigaban Æ™asar nan da jagoransu Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yake da shi.
A Æ™arshe ya ce yana fatan da yardar Allah jam’iyyar NDC.ce za ta kafa gwamnati a Æ™asar nan a zaÉ“en 2027, Æ™arÆ™ashin tikitin Obi/Kwankwaso.

No comments