Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Takarar Atiku A Jam'iyyar ADC Nasara Ce Ga Dukkan Masu Kishin Nijeriya -Ambasada Salga

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya na jam’iyyar ADC a ƙaramar hukumar Dala, Ambasada Abdurrahman M...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya na jam’iyyar ADC a ƙaramar hukumar Dala, Ambasada Abdurrahman Mainasara Salga, ya bayyana fitowar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, a matsayin nasara ga dukkan ‘yan Nijeriya masu kishin ci gaban ƙasa.

Salga ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai a Kano, inda ya ce nasar ta zo daidai lokacin da al’ummar ƙasar ke neman shugabanci nagari da zai magance matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da suka addabe ta.

“A matsayinsa na tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa mai gogewa a harkokin mulki, kuma mutum mai kishin ganin ‘yan Najeriya sun shawo kan matsin rayuwa, lokaci ya yi da masu jefa ƙuri’a za su yi tunani mai zurfi su zaɓi jam’iyyar ADC domin samun sauyi na gaskiya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa fitowar Atiku ta cancanci samun goyon bayan ‘yan Najeriya baki ɗaya, yana mai bayyana kyakkyawan fata cewa al’ummar ƙasar za su ba jam’iyyar ADC cikakken goyon baya a babban zaɓen 2027.

Haka kuma, Ambasada Abdurrahman Mainasara Salga ya yi kira ga dukkan ‘yan takar da suka fafata a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar a matakai daban-daban, ciki har da Majalisar Wakilai, Majalisar Dokokin Jihohi, Majalisar Dattawa da shugaban ƙasa, da su haɗa kai da waɗanda suka samu tikitin takara domin ƙarfafa jam’iyyar.

Ya jaddada cewa haɗin kai, haƙuri da sadaukarwa daga mambobin jam’iyyar ne ginshiƙin da zai tabbatar da nasar ADC a zaɓukan 2027.

“Nasarar ADC za ta samu ne kawai idan muka yi aiki tare da muradi ɗaya na ceto Najeriya daga halin da take ciki yanzu,” in ji shi.
 

No comments