Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara Ta Shirya Tallafa Wa Mata Da Masu Ƙaramin Ƙarfi Fiye Da Miliyan Ɗaya

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu naƙasa da sauran marasa galihu sama da miliyan ɗaya a faɗin ...

Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana shirinta na tallafa wa mata, ’yan mata, masu naƙasa da sauran marasa galihu sama da miliyan ɗaya a faɗin jihar, a wani mataki da ta ce zai ƙarfafa rayuwar al’umma tare da bunƙasa tattalin arziki.

An bayyana hakan ne a yayin wani taron kwana uku da aka gudanar a Sakkwato kan yadda za a aiwatar da Manufofin Ƙarfafa Tattalin Arzikin Mata na Ƙasa, wato Women’s Economic Empowerment Policy, a Jihar Zamfara cikin shekaru biyar masu zuwa.

Da take jawabi a wajen taron, Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma ta Jihar Zamfara, Dakta Aisha M.Z. Anka, ta ce shirin ya nuna ƙudurin gwamnatin jihar na tabbatar da cewa mata da sauran rukunin jama’a masu rauni sun samu damar inganta rayuwarsu.

Dakta Anka, wadda Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma, Alhaji Garba Aliyu Gayari, ya wakilta, ta bayyana cewa bunƙasa ilimin mata, kare haƙƙoƙinsu da kuma tabbatar da shigarsu cikin harkokin kuɗi zai taimaka wajen ƙarfafa iyalai da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa a al’umma.

Ta ce gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta nuna aniyarta ta bunƙasa rayuwar mata ta hanyar manufofi da shirye-shiryen da ke ƙarfafa shigarsu cikin ilimi, noma, kiwon lafiya da shugabanci na siyasa.

A cewarta, ba za a iya samun ci gaban tattalin arziki mai ma’ana ba tare da bai wa mata da ’yan mata damar cin gajiyar shirye-shiryen ci gaba ba.

“Mun na buƙatar ƙarin haɗin gwiwa daga Gwamnatin Tarayya, Bankin Duniya (World Bank) da sauran abokan hulɗar ci gaba domin tallafa wa matan Zamfara ta fuskar zamantakewa, siyasa da tattalin arziki domin samun ci gaba mai ɗorewa,” inji ta.

Ta kuma buƙaci mahalarta taron da suka haɗa da wakilan hukumomin gwamnati, cibiyoyin gwamnati, ƙungiyoyin fararen hula, sarakunan gargajiya da shugabannin addini da su bayar da gudunmawa mai amfani wajen daidaita manufofin da yanayin rayuwa, al’adu da dabi’un al’ummar Zamfara.

Tun da farko, wata ƙwararriyar mai ba da shawara da Shirin Kare Muhalli na Mata (WEP) ya ɗauka aiki, Misis Damaris Uja, ta ce an shirya taron ne domin ƙarfafa mata da matasa wajen samun damar amfani da haƙƙoƙinsu ta hanyar shirye-shiryen ci gaban muhalli, zamantakewa, siyasa da tattalin arziki.

Ta bayyana gurɓacewar muhalli, cin zarafin mata da rashin samun damar shiga harkokin kuɗi a matsayin manyan matsalolin da ke addabar mata da ’yan mata a sassa da dama na ƙasar nan.

A nasa jawabin yayin zaman nazari da tantance manufofin, jagorar taron, Farfesa Magdalyne Dura, ta ce aiwatar da manufofin wata alhakin gama-gari ce da ke buƙatar haɗin kan dukkan masu ruwa da tsaki.

Ta ce nasarar wannan tsari za ta dogara ne kan yadda masu ruwa da tsaki suka fahimci yanayin tattalin arziki da zamantakewar jihar tare da bayar da gudunmawa wajen samar da manufofin da za su dace da muradun al’ummar Zamfara.

Farfesa Dura ta kuma yi kira ga mahalarta taron da su tabbatar an tsara manufofin cikin tsarin da ya dace da al’adun gargajiya da kuma koyarwar addinin Musulunci da ake bi a jihar.

A ƙarshe, mahalarta taron sun gabatar da shawarwari daban-daban domin samar da cikakkiyar manufa ta ƙarfafa tattalin arzikin mata, wadda za ta magance buƙatun mata, ’yan mata, masu nakasa da sauran marasa galihu a Jihar Zamfara.
 

No comments