Bayanan da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar kwanan nan, sun nuna cewa Nijeriya ta kashe dala biliyan 2.34 wajen shigo da abinci daga ƙa...
Bayanan da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya fitar kwanan nan, sun nuna cewa Nijeriya ta kashe dala biliyan 2.34 wajen shigo da abinci daga ƙasashen waje a shekarar 2025.
An bayyana wannan adadi ne a cikin sabon rahoton ƙididdiga da CBN ya fitar kan yadda aka yi amfani da kuɗaɗen musayar ƙasashen waje a fannoni daban-daban na tattalin arziki.
Binciken bayyanan ya nuna cewa kuɗin da aka kashe wajen shigo da abinci a shekarar 2025 ya ragu idan aka kwatanta da dala biliyan 2.53 da aka kashe a shekarar 2024. Hakan na nufin an samu ragin dala miliyan 186.4, wanda ya yi daidai da kashi 7.37 cikin ɗari.
Duk da wannan ragi, alƙaluman sun nuna cewa shigo da abinci daga ƙasashen waje ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da buƙatar musayar kuɗaɗen ƙasashen waje, inda kuɗin da ake kashewa a kowane wata bai taɓa sauka ƙasa da dala miliyan 140 ba a tsawon shekarar.
Mafi yawan adadin kuɗin da aka kashe wajen shigo da abinci a shekarar 2025 ya fi yawa ne a watan Satumba, inda aka kashe dala miliyan 248.60.
Hakan kuwa ya biyo bayan watan Disamba da dala miliyan 245.86, sannan watan Yuli da dala miliyan 229.70.
A watan Afrilun 2025 ne aka kashe mafi ƙarancin kuɗin da bai wuce dala miliyan 141.13 ba, wato kusan daidai da dala miliyan 141.30 da aka kashe a watan Maris, 2025.
Ƙarin nazarin bayanan wanda CBN ya fitar, ya nuna cewa buƙatar shigo da abinci ta ƙaru a watannin Afrilu, Mayu da Yuni. Tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na shekarar 2025, Nijeriya ta kashe dala biliyan 1.07 wajen shigo da abinci, yayin da aka kashe dala biliyan 1.28 tsakanin watan Yuli zuwa Disamba, duk a cikin 2025.
Wannan na nufin cewa kashi 54.55 cikin ɗari na jimillar kuɗin da aka kashe wajen shigo da abinci a shekarar 2025 an kashe su ne a farkon tsakiyar shekarar.
Idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, wato 2024, za a ga cewa kuɗin da aka kashe wajen shigo da abinci ya ragu sosai a watannin Fabrairu, Maris da Agusta. A watan Fabrairu, kuɗin ya ragu da kashi 35.61 cikin ɗari daga dala miliyan 303.91 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 195.68 a shekarar 2025.
Haka kuma a watan Maris ya ragu da kashi 36.22 cikin ɗari daga dala miliyan 221.54 zuwa dala miliyan 141.30.
Sai dai wasu watanni sun nuna ƙaruwa. A watan Yuli, kuɗin ya ƙaru da kashi 53.23 cikin ɗari daga dala miliyan 149.91 a shekarar 2024 zuwa dala miliyan 229.70 a shekarar 2025.
Haka kuma watan Janairu ya nuna ƙaruwar kashi 29.61 cikin ɗari daga dala miliyan 164.43 zuwa dala miliyan 213.11.
Bayanan sun ci gaba da nuna cewa duk da raguwar kuɗaɗen musayar ƙasashen waje da ake kashewa wajen shigo da abinci a shekarar 2025, har yanzu Nieriya na matuƙar dogaro da kayan abinci da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, lamarin da ke jefa masu amfani da kayayyaki cikin matsin-lambar canjin kuɗi da kuma sauye-sauyen farashin kayan masarufi a kasuwannin duniya.
Shugaban Kungiyar Masu Ƙananan Sana'o'i na Nijeriya (Association of Small Business Owners of Nigeria), Femi Egbesola, ya bayyana a baya cewa rashin tsaro da ƙarancin amfani da fasahar zamani a harkar noma na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke sa Nijeriya ci gaba da dogaro da shigo da abinci daga ƙasashen waje.
Egbesola ya ce:
“Yawancin manoma sun daina zuwa gonakin su saboda matsalar rashin tsaro. An yi watsi da gonaki da dama. A can ne ake samar da kayan amfanin gona na farko. Lokacin da manoma suka noma suka girbe ne masana’antu da sauran masu amfani ke samun damar sayen amfanin gona domin amfani da su a matsayin albarkatun ƙasa. A yanzu kuwa an ƙaurace wa gonaki da dama saboda matsalar tsaro.”
Ya ƙara da cewa yawan amfanin gona a Nijeriya har yanzu yana ƙasa da matakan da ake samu a duniya saboda amfani da tsofaffin kayan aiki na gargajiya da hanyoyin noma marasa inganci. Ya buƙaci gwamnati ta haɗa fasahar zamani da harkar noma, ta samar da ingantattun kayan aiki ga ƙananan manoma, sannan ta ƙara saka hannun jari a fannin sarrafa noma da injina domin rage giɓin da ke akwai wajen samar da abinci.

No comments