Daga Zubairu Lawal, Lafia Dan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa mai wakiltar mazabar Lafia ta Tsakiya a ƙarƙashin Jam’iyyar A...
Dan takarar kujerar Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa mai wakiltar mazabar Lafia ta Tsakiya a ƙarƙashin Jam’iyyar APC, Barrista Abubakar Imam Zanwa, ya bayyana cewa idan aka zaɓe shi, zai gabatar da kudirin doka na kashin kai domin samar da dokokin da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
Barrista Abubakar Zanwa ya yi nuni da yadda Hukumar Bunƙasa Birane ta Jihar Nasarawa (NUDB) ke aiki a faɗin jihar, yana mai cewa Lafia na samun ci gaba cikin sauri saboda yawaitar mutanen da ke ƙaura zuwa babban birnin daga sassa daban-daban na rayuwa.
Ya ce:“Lokacin da muke Jihar Plateau, akwai Hukumar Bunƙasa Birnin Jos (Jos Metropolitan Development Board).
Don haka yanzu muna buƙatar Hukumar Bunƙasa Birnin Lafia (Lafia Metropolitan Development Board) wadda za ta kawo ci gaba cikin gaggawa domin kauce wa matsalolin da ke tattare da karuwar jama’a.
Haka kuma, za ta tabbatar da tsara birnin yadda ya kamata bisa tsarin mallakar ƙasa a dukkan sassan garin.
Idan muka samu ingantaccen tsarin babban birni (master plan) na Lafia da kuma tsare-tsaren ci gaba na matsakaici da na dogon lokaci, za mu cimma manufofin da muka sa gaba.”
Ya ƙara da cewa: “A hakikanin gaskiya, muna buƙatar ci gaba mai tsari. Dole ne a samar da gine-gine da kayayyakin more rayuwa domin karɓar da kuma samar wa waɗannan mutane masauki.
Hakan zai sa birnin ya yi daidai da sauran biranen da suka ci gaba.”
A cewarsa, Hukumar Bunƙasa Birane ta Jihar Nasarawa (NUDB) tana da nauyin kula da tsarin gine-gine da bunƙasa birane a duk faɗin jihar, ciki har da ƙananan hukumomi 13.
Ya ce kasancewar Lafia babban birni ne da ke karɓar mutane masu yawa, akwai buƙatar kafa hukuma ta musamman irin ta Hukumar Tsare-tsaren Ci Gaban Karu (KAPDA).
Barrista Zanwa, wanda tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ne kuma tsohon Kwamishinan Harkokin Musamman, ya bayyana cewa babban aikin ɗan majalisa shi ne yin doka.
Ya kuma yi alkawarin bayar da wakilci mai inganci idan aka sake ba shi dama a zaɓen shekarar 2027.
“Ni lauya ne ta fuskar sana’a kuma ɗan siyasa. Na wakilci mazabar Lafia ta Tsakiya daga shekarar 2015 zuwa 2019 a Majalisa ta Biyar. A lokacin, na gabatar da wasu kudurorin dokoki na kashin kai, ciki har da Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka (Administration of Criminal Justice Law) wadda ke aiki a yanzu kuma ta taimaka wajen sauƙaƙa tsarin shari’ar laifuka.
Haka kuma, mun samar da Dokar Zaɓen Ƙananan Hukumomi wadda ta sauƙaƙa tsarin zaɓe da zaɓar shugabanni a matakin ƙananan hukumomi. Mun kuma samar da Dokar Ƙananan Hukumomin Jihar Nasarawa.”
Ya ci gaba da cewa: “Dokar Ƙananan Hukumomin Jihar Nasarawa tana kula da harkokin gudanarwa da kuɗaɗen ƙananan hukumomi.
A cikin dokokin da muka samar akwai wasu muhimman tanade-tanade da suka magance matsalolin da suka shafi wa’adin shugabannin ƙananan hukumomi. A baya ana ta samun ce-ce-ku-ce kan wa’adin shekara ɗaya, biyu ko uku.
Na dauki nauyin kudirin dokar da ya soke tsofaffin dokoki tare da samar da sabbin dokoki da suka kayyade wa’adin shekaru uku ga shugabannin ƙananan hukumomi.”
Zanwa ya kuma bayyana cewa Jihar Nasarawa na daga cikin jihohin da suka fi jan hankalin masu zuba jari a Najeriya, sakamakon manufofin da Gwamna Abdullahi Sule ya aiwatar.

No comments