Ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Iƙamatus Sunnah ta ƙalubanci masarautar Zazzau game da wasu masallatan ta guda takwas da ta ce ...
Ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'a Wa Iƙamatus Sunnah ta ƙalubanci masarautar Zazzau game da wasu masallatan ta guda takwas da ta ce masarautar ta rufe mata ba bisa ƙa'ida ba, inda ta zayyano wasu sharuɗɗa da idan masarauyar ba ta cika su ba, to za su haɗu a gaban ƙuliya.
A cikin wata takardar gargaɗi da jaridar MATATTARAR LABARAI ta ci karo da ita, wace ta fito daga ofishin Lauyoyin na A.T Abubakar & Associates, wacce kuma aka aika zuwa ga Sakataren masauratar, an bayyana cewa a gaggauta a buɗe masallatan guda 8 da masarautar Zazzau ɗin ta rufe a ciki da wajen Lardin Zariya.
Izala, ta hannun Lauyoyin nata, ta bayyana cewa masarautar Zazzau ta tauye mata haƙƙi na 'yancin yin ibada, da'awa, karantarwa tare kuma da nuna wariya ga 'yan Izala, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.
Lauyoyin na Izala sun kuma bayyan cewa; babu wata dokar ƙasa da ta bai wa Sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Bamalli da masarauta ikon hanawa, kula da addinai ko hana gudanar da wasu masallatai mallakin 'yan ƙasa nagari, domin masautar ba gwamnati ba ce. Don haka ƙungiyar Izala ta bai wa Sarkin Zazzau da masarautar kwanaki 30 su buɗe dukkan masallatan ta guda 8 da aka rufe ko ta ɗauki matakin Shari'a.
Sharuɗɗan da Izalar ta bai wa masarautar Zazzau ɗin, sun haɗa gaggauta buɗe waɗannan masallatai guda takwas ba tare da wasu sharuɗɗa ba.
Janye duk wata doka, ko umurni, ko wata takarda da aka bayar na hana amfani da masallatan Izala ko na wata ƙungiyar musulmi a Zariya da kewaye.
Rubutacciyar takarda daga masarautar, ko wata Hukuma, mai nuna cewa za a girmama damar da Izala ke da ita na gudanar da ibada, tare da ba ta kariyar da tsarin mulki ya tanada
A ƙarshe, wajibi ne a kiyaye kyara ko musgunawa a duk lokacin da Izala ke gudanar ayyukan ta na ibada.
Waɗannan ne sharuɗɗan da Layoyin suka bayyana cewa idan masarauyar ba ta cika su ba, to za su haɗu da Izala a gaba ƙuliya.
Lauyoyin na Izala sun aika kwafin wannan takardar gargaɗi zuwa ga ofishin gwamnan jihar Kaduna, ofishin kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, ofishin jami'an tsaron farin kaya na DSS, ofishin jami'in 'yan sandan yankin Zariya (DPO), shuganan ƙungiyar Izala na Zariya, shugaban kwamitin amintattu na Atta'awun Islamic Trust.
Ya zuwa kammala wannan labari dai, MATATTARAR LABARAI ba ta samu wani martani daga Masarautar ta Zazzau ba.




No comments