Dakarun Operation Fansan Yanma sun samu nasarar ceto matar marigayi Janar Rabe Abubakar bayan wani farmaki da suka kai a inda 'yan bindi...
Duk da an samu ceto matar, amma rahotanni sun nuna cewa sakamakon musayar wuta da aka yi tsakanin sojoji da ‘yan bindigar, sai da 'yan bindigar suka harbi matar, kafin su tsere.
Rahotannin sun nuna cewa an kai masu wannan farmakin ne a ƙauyen Tunga, inda Rundunar sojojin ta ce ana ci gaba da farautar ‘yan bindigar ƙarƙashin Operation Clean Sweep III a yankin Matazu.
Daraktan yaɗa labarai na tsaron ƙasar nan,
Manjo Janar Samaila Uba, ya bayyana cewa an samu wannan nasara ce a sakamakon bincike da da kuma kai ɗauki, wanda dakarun shirin Operation FASAN YAMMA suka aiwatar.
Ya ce, jami'an sojin sun tsananta hare-hare a daidai inda waɗannan miyagu, wanda ya kai ga gano daidai inda suke a ƙauyen Tunga.
Janar Samaila ya ce, bayan da aka samu nasarar ceto matar ne, sai aka garzaya da ita wani asibitin sojoji don ba ta kulawar gaggawa ta magani, wanda kuma yanzu haka tana farfaɗowa daga halin da ta shiga.
Wata majiyar ta shaida cewa yanzu haka jami'an tsaron suna can suna tsananta bincike don kamo waɗannan 'yan ta'adda a duk inda suke.
Majiyoyin sojoji sun sanarwa Zagazola Makama cewa jami’an tsaro sun yi nasarar gano maboyar maharan ne bayan samun bayanan sirri kan inda suke boye.

No comments