Daga Zubairu Lawal Lafia Ɗan takarar Sanata na jam’iyyar mai mulki ta APC, Alhaji Halilu Emvulanza, ya bayyana cewa da yardar Allah za a ra...
Ɗan takarar Sanata na jam’iyyar mai mulki ta APC, Alhaji Halilu Emvulanza, ya bayyana cewa da yardar Allah za a rantsar da shi a ranar 20 ga Yuni, 2027 a matsayin zaɓaɓɓen Sanatan da zai wakilci Mazabar Sanatan Nasarawa ta Arewa a Jihar Nasarawa.
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da zaɓaɓɓun ‘yan jarida a Nasarawa Eggon, jim kaɗan bayan bikin naɗa sabon Aren Eggon da aka gudanar a ranar Asabar a gidansa da ke Nasarawa Eggon, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Nasarawa Eggon.
Ya kuma bayyana cewa idan aka zaɓe shi a matsayin mamba na Majalisar Dattawa, zai ci gaba da ayyukan jin ƙai da hidimtawa al’umma.
“Ina tabbatar muku cewa tun tsawon rayuwata an san ni da yi wa al’umma hidima da taimakon jama’a,” in ji shi.

No comments