Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Ɗaga Likafar Abdul'aziz Abdul'aziz A Matsayin Babban Mataimaki Na Musamman Kan Yaɗa Labarai

  Bisa nuna ƙwazo da jajircewa a aiki, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗaga likafar Abdul'aziz Abdul'aziz daga Mataimaki na musam...


 
Bisa nuna ƙwazo da jajircewa a aiki, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗaga likafar Abdul'aziz Abdul'aziz daga Mataimaki na musamman, zuwa matsayin Babban Mataimaki na Musamman kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a (Senior Special Assistant on Media and Public Enlightenment).

Wannan naɗi ya kasance abin alfahari da kuma nuna amincewa da Shugaba Tinubu ya yi bisa gudumawar da Abdul'aziz ke bayarwa a cikin harkar sadarwa da yaɗa labarai ta Fadar Shugaban Ƙasa da kuma ta ƙasa baki ɗaya.

Da ya ke nuna jin daɗin sa bisa wannan ci gaba, Malam Abdul'aziz ya bayyana cewa sabon naɗin ya ƙara masa nauyin aiki da ƙalubalen da ke buƙatar ƙarin jajircewa, ƙwazo da sadaukarwa wajen gudanar da ayyukan sa.

Daga nan ya miƙa godiyar sa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da nuna masa ƙauna da amincewa, tare da gode wa shugabannin sa da abokan aikin sa da ke fannin sadarwa bisa haɗin kai, jagoranci da hangen nesa da suke rabawa.

Haka kuma, ya nuna matuƙar godiya ga abokan aikin sa, takwarorin sa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai, inda ya ce gudumawar da suka bayar ta taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin da ya samu a aikin sa.

Abdul'aziz Abdul'aziz ya bayyana cewa ya karɓi takardar tabbatar da sabon naɗin nasa, wanda ya zo daidai da sabon tsarin aikin sa kamar yadda Shugaban Ƙasa ya amince tun ranar 23 ga Afrilu, 2026.

No comments