Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Ya Ƙaddamar Da Gidajen Alƙalan Kotunan Ɗaukaka Ƙara, Ya Buƙaci Jihohi Su Ma Su Yi Ƙoƙari Wajen Inganta Bangaren Shari'a

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabbin gidaje guda 10 na Alƙalan Kotunan Ɗaukaka Ƙara a Unguwar Katampe, Abuja, inda ya sake ...

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabbin gidaje guda 10 na Alƙalan Kotunan Ɗaukaka Ƙara a Unguwar Katampe, Abuja, inda ya sake jaddada ƙudurin gwamnatin sa na ƙarfafa bangaren shari’a da tabbatar da ‘yancin sa.

 Shugaban, wanda Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayyan Nijeria, Lateef Fagbemi, ya ce aikin wani muhimmin zuba jari ne wajen tabbatar da doka da inganta dimokuradiyya. Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin shari’a ba wai yana buƙatar kulawa da dokoki da Alƙalai kaɗai ba, har ma da ababen more rayuwa da muhalli mai kyau.

Tinubu ya ce samar da gidaje masu tsaro da inganci ga alkalai zai kara musu kwarin gwiwa da inganta aikin shari’a, yana mai jaddada cewa jin dadin su zuba jari ne ga kasa baki daya.

Ya kuma buƙaci gwamnatocin jihohi su yi koyi da gwamnatin tarayya ta hanyar ƙara zuba jari a bangaren shari’a, yana mai cewa nauyin tallafa wa kotuna ba na gwamnatin tarayya kaɗai ba ne.

A nasa bangaren, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce samar da irin wadannan ababen more rayuwa yana kara karfafa ‘yancin bangaren shari’a ne, ba rage shi ba.

Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen samar da ingantaccen muhalli ga alkalai, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta aikin shari’a da kare martabar bangaren.

An ƙaddamar da aikin ne kwana daya bayan bude sabon ginin Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, wanda ke nuna yadda gwamnati ke mai da hankali kan bunkasa bangaren shari’a.




 

No comments