Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Akwai Matuƙar Buƙatuwar Kafofin Yaɗa Labarai Da Hukumomin Tsaro Su Ƙarfafa Haɗin Gwiwa Don Kare Zaman Lafiya -Minista

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga kafofin yaɗa labarai da hukumomin tsaro da su ƙara ƙarfafa haɗin...


Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga kafofin yaɗa labarai da hukumomin tsaro da su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa a matsayin wata muhimmiyar hanya ta kare tsaron ƙasa, ƙarfafa amincewar jama'a, da kuma ci gaba da gina ƙasa.

Da yake jawabi a matsayin shugaban taro kuma babban mai masaukin baƙi a Taron Ƙoli kan Tsaro na Ƙasa wanda Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ta shirya tare da haɗin gwiwar Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) a Abuja ranar Alhamis, Ministan ya bayyana cewa alaƙar da ke tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro tana da muhimmanci matuƙa wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da cigaban ƙasa.

Da yake magana kan taken taron, wato, "Kafofin Yaɗa Labarai da Hukumomin Tsaro a Matsayin Abokan Hulɗa Wajen Gina Ƙasa," Idris ya ce duka ɓangarorin biyu suna da muhimmiyar rawa a tsarin cigaban ƙasa kuma suna da alhakin kare muradun ƙasa.

Ya ce, "Yayin da aka ɗora wa hukumomin tsaro alhakin kare rayuka, dukiyoyi da ikon mallakar ƙasa, kafafen yaɗa labarai kuwa su ne masu sanya ido kan al'umma, dandalin musayar ra'ayoyi kuma su zama gada tsakanin gwamnati da al'umma. 

"Dukkanin su suna da buri guda ɗaya, wato kare muradun ƙasa tare da inganta zaman lafiya, haɗin kai da cigaba."

Ministan ya jaddada cewa ingantaccen haɗin gwiwa wanda aka gina bisa mutunta juna, ƙwarewa a aiki, amincewa da fahimtar rawar da kowane ɓangare yake takawa za ta ƙara ƙarfafa tsaron ƙasa tare da haɓaka amincewar jama'a ga cibiyoyin gwamnati.

Ya bayyana cewa Nijeriya, kamar sauran ƙasashe na duniya, tana fuskantar ƙalubalen tsaro masu sarƙaƙiya da suka haɗa da ta'addanci, tsattsauran ra'ayi na tashin hankali, laifukan yanar gizo, aikata manyan laifuka, yaɗa bayanan ƙarya, yunƙurin ɓallewa da sauran sababbin barazanar tsaro waɗanda ke buƙatar haɗin kai da dabarun magance su.

A cewar sa, gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta sanya tsaro a matsayin ginshiƙi mai muhimmanci a cikin Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta hanyar amfani da dabaru daban-daban da suka haɗa da ayyukan soji, tattara bayanan sirri, haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, amfani da sababbin fasahohi da kuma haɗa al'umma cikin ayyukan tsaro.

Ya ce, "Mun fahimci cewa babu wata ma'ana ta cigaba ba tare da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. Saboda haka gwamnati ta rungumi cikakkiyar dabarar tsaro wadda ta haɗa da aikin soji, tattara bayanan sirri, haɗin gwiwa tsakanin hukumomi, amfani da fasahar zamani da kuma haɗin kai da al'umma."

Ministan ya bayyana nasarorin da hukumomin tsaro suka samu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu, ciki har da hallaka da kama 'yan ta'adda, 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka, rusa sansanoni da maɓoyar masu laifi, da kuma ceto ɗaruruwan mutanen da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ya ce hare-haren soji da ake ci gaba da kaiwa sun rage ƙarfin ƙungiyoyin 'yan ta'adda a Arewa-maso-gabas, yayin da ƙarin matakan yaƙi da 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane a Arewa-maso-yamma da Arewa-ta-tsakiya suka samar da sakamako mai kyau.

Idris ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta zuba jari sosai wajen samar da kayan aikin soji na zamani, cibiyoyin tattara bayanan sirri, fasahohin sa-ido da kuma horar da jami'an tsaro domin ƙara inganta ayyukan su da kuma ƙarfafa ikon ƙasar wajen tinkarar sababbin barazanar tsaro.

Baya ga ayyukan tsaro, Ministan ya ce gwamnatin Tinubu tana ci gaba da magance tushen matsalolin rashin ppptsaro ta hanyar sauye-sauyen tattalin arziki, shirye-shiryen ƙarfafa matasa, gina ababen more rayuwa, samar da damar ilimi da aiwatar da shirye-shiryen jin daɗin al'umma domin bunƙasa rayuwar jama'a da samar da wadata mai ɗorewa.

Da yake magana kan rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa, Idris ya jaddada cewa aikin jarida na gaskiya da rikon amana ya zama mafi muhimmanci a wannan zamani da bayanan ƙarya, labaran bogi da yaɗa bayanan da ba su da tushe ke bazuwa cikin sauri ta hanyoyin sadarwa na zamani.

Ya ce, "Ba a kare tsaron ƙasa idan aka yaɗa bayanan da ba a tantance su ba. Haka kuma ba a kare shi idan aka yi biris da halastattun damuwar jama'a. Ƙalubalen da ke gabanmu shi ne samar da daidaito tsakanin 'yancin jama'a na samun bayanai da kuma wajabcin kare tsaron ƙasa."

Ministan ya buƙaci 'yan jarida da su ci gaba da kiyaye ƙa'idojin ƙwarewa, sahihanci, adalci da ɗabi'ar aikin jarida, yayin da ya ƙarfafa hukumomin tsaro su ƙara kusanci da kafafen yaɗa labarai ta hanyar samar da bayanai cikin lokaci, gaskiya da kuma bayyananniyar hanya.

Ya tabbatar wa mahalarta taron cewa Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta ci gaba da inganta kyakkyawar hulɗa tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro ta hanyar tattaunawa, horaswa, sadarwa mai inganci da shirye-shiryen wayar da kan jama'a.

Da yake bayyana cewa tsaro nauyi ne na kowa, Idris ya yi kira ga 'yan ƙasa, al'ummomi, ƙungiyoyin fararen hula, cibiyoyin gargajiya, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki da su ba da tasu gudunmawa wajen gina Nijeriya mai zaman lafiya, haɗin kai da wadata.

Ya yaba wa Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) da Hukumar Tsaro ta DSS bisa shirya taron, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa shawarwarin da za su fito daga taron za su ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai da hukumomin tsaro domin cimma manufofin tsaron ƙasa.

Taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnati, shugabannin hukumomin tsaro, shugabannin kafafen yaɗa labarai, ƙwararrun masu hulɗa da jama'a da sauran masu ruwa da tsaki. 

Daga cikin waɗanda suka halarta akwai Darakta Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Sufeto Janar na 'Yan Sanda wanda Mataimakin Sufeto Janar Miller Ɗantawaye ya wakilta; Shugaban Hukumar NDLEA wanda Mataimakin Babban Kwamandan Miyagun Ƙwayoyi Dankolo Shehu Mohammed ya wakilta; Shugaban Cibiyar Hulɗa da Jama'a ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku; da Shugaban Ƙungiyar 'Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahaya, tare da sauran manyan baƙi daga ɓangarorin gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kan su.


 

No comments