Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Jakadun Afrika Suka Tarbi Sabon Jakadan Nijeriya, Mahmood Yakubu A Doha Ta Ƙasar Ƙatar

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya fara aiki a matsayin Jakaden Tarayyar Nijeriya a ƙa...


Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya fara aiki a matsayin Jakaden Tarayyar Nijeriya a ƙasar Ƙatar.

Jakada Yakubu ya isa babban birnin ƙasar, Doha a ranar Laraba, inda Daraktan Sashen Ladabi na Ma'aikatar Harkokin Wajen Ƙatar, Jakada Ibrahim Yousif Abdullah Fakhro, ya tarbe shi cikin girmamawa a filin jirgin sama. 

Haka kuma, jakadun ƙasashen Afrika 13 ne suka yi masa maraba tare da Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Iskar Gas (GECF), Dakta Philip Mshelbila, da Shugaban Ƙungiyar 'Yan Nijeriya Mazauna Ƙasashen Waje (NIDO) reshen Ƙatar, Mista Michael Ndukaihe Ihekwaba.

Yakubu ya tafi wannan sabon aiki na diflomasiyya da tarihin nagartaccen aikin gwamnati. A matsayin sa na Shugaban INEC daga shekarar 2015 zuwa 2025, ya jagoranci manyan sauye-sauye a tsarin zaɓen Nijeriya, waɗanda suka ƙarfafa tsarin gudanar da zaɓe, suka inganta amfani da fasaha a harkokin zaɓe, suka bunƙasa tsarin tantance masu kaɗa ƙuri'a, tare da ƙara amincewar jama'a ga cibiyoyin dimokiraɗiyya.

Ana girmama Ambasada Yakubu sosai saboda jajircewar sa wajen tabbatar da gaskiya, ƙwarewa, da kuma kyakkyawan shugabanci na dimokiraɗiyya. 

A lokacin jagorancin sa, ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da zaɓuɓɓukan ƙasa da na cike gurbi cikin nasara.

Naɗin sa a matsayin Jakaden Nijeriya a Ƙatar yana nuna irin amincewar da Gwamnatin Tarayya take da ita ga jagorancin sa, gogewar sa da kuma ƙwarewar sa wajen inganta muradun Nijeriya na diflomasiyya, tattalin arziki da dangantakar ƙasashe a ɗaya daga cikin muhimman ƙasashen Gabas ta Tsakiya.

Ana sa ran zai ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da Ƙatar, musamman a fannoni kamar kasuwanci, zuba jari, makamashi, ilimi da kuma hulɗar al'ummomin ƙasashen biyu.


 

No comments