Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Yaba Wa Dakarun Tsaro Kan Kashe Ɗan Bindiga Ibrahim Bastuje, Da Ceto Matar Marigayi Janar Rabe

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa rundunar sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro bisa nasarar da suka samu a wani samame da ak...

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa rundunar sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro bisa nasarar da suka samu a wani samame da aka gudanar a Jihar Kogi, wanda ya kai ga kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga, Ibrahim Bastuje.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Litinin, Tinubu ya bayyana wannan nasara a matsayin wani babban koma baya ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da suka daɗe suna addabar al’ummomi a Kogi da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Shugaban ƙasar ya ce Bastuje ya yi kaurin suna wajen jagorantar hare-hare, sace-sacen mutane da sauran ayyukan ta’addanci da suka jefa mazauna yankunan cikin wahala da fargaba.

Ya ce kashe shi zai taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali tare da ƙarfafa gwiwar al’umma kan cewa hukumomin tsaro na ci gaba da samun nasara a yaƙin da suke yi da masu aikata laifuka.

“Ina taya jaruman dakarunmu murnar wannan gagarumar nasara. Najeriya ba za ta miƙa ko da inci ɗaya na ƙasarta ga masu laifi ba. Duk wanda ya zaɓi hanyar tada hankali da zubar da jinin bayin Allah, ba zai samu mafaka ba. Wannan nasara ta nuna ƙudurin jami’an tsaronmu na tabbatar da tsaro a ko’ina cikin ƙasar nan,” in ji Tinubu.

Hakazalika, shugaban ƙasar ya yaba wa jami’an tsaron kan nasarar da suka samu wajen ceto Hajiya Amina Rabe Abubakar, matar marigayi tsohon Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Tsaro, Janar Rabe Abubakar mai ritaya.

Tinubu ya ce ceto ta cikin koshin lafiya ya nuna ƙwarewa, jajircewa da haɗin gwiwar da jami’an tsaro ke nunawa wajen yaƙi da masu aikata miyagun laifuka.

“Dawowar Hajiya Amina gida cikin aminci abin farin ciki ne ga iyalanta da kuma daukacin ’yan Najeriya. Ina yaba wa jami’an da suka shirya tare da aiwatar da wannan aiki cikin nasara. Hakika muna bin dakarunmu bashin godiya saboda sadaukarwar da suke yi kullum domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji shugaban ƙasar.

Tinubu ya kuma tabbatar wa ’yan Nieriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da samar wa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro kayan aiki, horo da tallafin da suke bukata domin kawo ƙarshen matsalolin ’yan bindiga, satar mutane da sauran nau’o’in aikata laifuka a ƙasar.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro haɗin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen yaƙi da rashin tsaro.
 

No comments