Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sojojin Nijeriya Sun Lallasa 'Yan Ta'addan Lakurawa a Kebbi, Sun Ƙwace Makamai da Bamabamai

Dakarun Soji na Sashe na biyu na oferashan FANSAN YAMMA da ke aiki a Jihar Kebbi sun kwato tarin manyan makamai  da kuma bama-bamai (IEDs), ...

Dakarun Soji na Sashe na biyu na oferashan FANSAN YAMMA da ke aiki a Jihar Kebbi sun kwato tarin manyan makamai  da kuma bama-bamai (IEDs), a wani ci gaba da ƙoƙari  da nufin kawar da ta’addanci da sauran ayyukan miyagun laifuka a yankin Arewa maso Yamma.

An gudanar da wannan farmaki ne a ranar 14 ga Yuni, 2026, a yankin Dogon Daji da ke Ƙaramar Hukumar Dandi ta jihar. A yayin farmakin, jaruman dakarun sun yi amfani da ƙarfin wuta mai yawa wajen murƙushe ƙungiyar ‘yan ta’addan Lakurawa, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga wajen.

A ci gaba da bin sawun ‘yan ta’addan da suka gudu ya kai ga gano da kwato dimbin makamai, bama-bamai da kayan aiki da suka bari a baya yayin tserewar su.

Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya ce kayan da aka kwato daga sansanin ‘yan ta’addan sun haɗa da bututun harba roka (RPG), rokokin yaƙi da dama da ake sama bututun harba roka (warheads), bama-bamai na gida (IEDs) masu yawa, babura guda biyu da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen kai hari, caja na batura, da wasu kayayyakin su na kashin kai. Ya ƙara da cewa dakarun sun kammala wannan fafatawa lafiya lau, ba tare da samun asara ko jikkata ba.

Ya kuma jaddada cewa wannan nasara na nuna ƙudirin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso Yamma, oferashan FANSAN YAMMA, na rushe hanyoyin ‘yan ta’adda da ‘yan fashi da makami a yankin. A cewarsa, Rundunar Sojin Najeriya za ta ci gaba da matsa lamba kan wadannan miyagun, tare da hana su damar gudanar da ayyukansu domin tabbatar da tsaro da lafiyar al’umma masu bin doka.


 

No comments