Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da manhajar sauya tsarin watsa shirye-shiryen talbijin daga analog zuwa dijital (Digital Switch Over – DSO), i...
A taron ƙaddamarwar wanda aka yi a hedikwatar Kamfanin Satalayit na Sadarwa na Nijeriya (NIGCOMSAT) da ke Abuja a ranar Laraba, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce: "Idan aka aiwatar da tsarin DSO gaba ɗaya, zai samar da ayyukan yi, ya ƙarfafa masana'antun cikin gida, ya faɗaɗa isar shirye-shirye ga jama'a, ya bunƙasa samar da abun ciki, ya ƙara damar talla tare da samar da sababbin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ga gidajen watsa shirye-shirye da masu samar da shirye-shirye cikin gida."
Ministan ya ce ƙaddamar da wannan manhaja wata muhimmiyar alama ce a tarihin harkar watsa shirye-shirye a Nijeriya, kuma tana nuna jajircewar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen kawo sauyi ta fuskar fasahar zamani, bunƙasa tattalin arziki, ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire da samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a ƙasar nan.
Ya ce, "Aikin DSO ba sauyin fasaha kawai ba ne, wani muhimmin mataki ne na zamanantar da harkar watsa shirye-shirye a Nijeriya."
Idris ya bayyana cewa wannan nasara ta samu ne bisa goyon baya da jagorancin Shugaba Tinubu, wanda Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta mayar da hankali sosai kan sauyin fasahar zamani, bunƙasar tattalin arziki, ƙirƙire-ƙirƙire da samar da muhimman kayayyakin more rayuwa.
Ya ce: "Wannan ƙaddamarwa ba wata nasara ce ta harkar watsa shirye-shirye kaɗai ba; wani ɓangare ne na ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya na gina Nijeriya mai haɗin kai, mai gogayya da sauran ƙasashe, kuma mai yalwar arziki."
Ministan ya bayyana cewa kwana guda kafin ƙaddamar da DSO ɗin, an gudanar da tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki a sassa daban-daban na harkar watsa shirye-shirye, ciki har da gidajen talbijin da na rediyo, masu rarraba sigina, masu ƙera na'urorin dikoda, masu samar da shirye-shirye, NIGCOMSAT, DigiTeam, Ƙungiyar Masu Watsa Shirye-shirye ta Nijeriya (BON), Hukumar Kula da Talla ta Nijeriya (ARCON) da sauran masu ruwa da tsaki.
A cewar sa, duk da bambance-bambancen ra'ayi a wasu fannoni, masu ruwa da tsakin sun sake tabbatar da aniyar su ta ganin an aiwatar da shirin cikin nasara.
"Abu ɗaya da ya fito fili daga wannan tattaunawa shi ne cewa dukkan masu ruwa da tsaki sun haɗa kai wajen tabbatar da nasarar aiwatar da shirin DSO a Nijeriya," inji shi.
Idris ya yi magana kan damuwar da ake bayyanawa game da aiwatar da shirin DSO ɗin, yana mai cewa ba manufar shirin ba ce ta maye gurbin wata fasaha da wata, illa dai faɗaɗa damar samun shirye-shirye tare da rungumar sababbin hanyoyin isar da su.
Ya ce, "Har yanzu 'Digital Terrestrial Television' (DTT) wani muhimmin ɓangare ne na tsarin watsa shirye-shiryen dijital na Nijeriya. Abin da muke nema shi ne tsarin haɗaka wanda zai haɗa DTT da tsarin tauraron ɗan'adam kai-tsaye zuwa gida (Direct-to-Home) da kuma manhajojin dijital."
Ministan ya sake jaddada aniyar gwamnati ta tallafa wa fasahar cikin gida, ƙarfafa masana'antun Nijeriya da kuma tabbatar da cewa masu ƙirƙirar shirye-shirye na cikin gida suna ci gaba da kasancewa a tsakiyar tsarin harkar watsa shirye-shirye.
"Dole ne DSO ya samar da damarmaki ga 'yan kasuwar Nijeriya, masu ƙirƙire-ƙirƙire da kuma ma'aikatan Nijeriya," inji shi.
Ya yaba wa hukumomin NIGCOMSAT, NBC, BON, ARCON, DigiTeam, gidajen watsa shirye-shirye, masana'antun cikin gida da sauran masu ruwa da tsaki saboda gudunmawar da suka bayar, yana mai cewa wannan ƙaddamarwar da aka yi ita ce matakin farko na wani sabon zamani a harkar watsa shirye-shirye a Nijeriya.
Daga nan sai Ministan ya ƙaddamar da manhajar 'Digital Switch Over' a hukumance a madadin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Ministan Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Dijital, Dakta Bosun Tijani, ya bayyana DSO a matsayin wani babban mataki a tafiyar Nijeriya ta sauyin fasahar zamani.
Ya ce wannan shiri yana nuna aniyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta saka hannun jari a muhimman kayayyakin more rayuwa na dijital da za su samar da cigaban tattalin arziki na dogon lokaci.
Ya ce: "DSO yana daga cikin sakamakon farko da ake gani na dabarun mu na gina muhimman kayayyakin fasahar dijital da nufin samar da tattalin arzikin da ya kai dala tiriliyan ɗaya."
Dakta Tijani ya bayyana cewa an yi shirin shimfiɗa kilomita 90,000 na igiyoyin 'fibre-optic' a faɗin ƙasar nan, tare da amincewar Shugaban Ƙasa ta hanyar ƙaddamar da wasu ƙarin satalayit guda biyu domin ƙarfafa sadarwa a Nijeriya.
A jawaban su daban-daban, Darakta Janar na Hukumar Kula da Gidajen Watsa Shirye-shirye ta Nijeriya (NBC), Charles Ebuebu, da Manajar Darakta kuma Babbar Jami'ar Gudanarwa ta NIGCOMSAT, Jane Egerton-Idehen, sun bayyana ƙaddamar da DSO ɗin a matsayin farkon wani sabon zango a harkar watsa shirye-shirye.
Ebuebu ya ce: "Wannan ya fi zama manhajar talbijin kawai; wata babbar manhajar sadarwa ce ta ƙasa da aka tsara domin faɗaɗa damar samun bayanai, ilimi da damarmakin dijital ga dukkan 'yan Nijeriya."
Ita kuwa Egerton-Idehen cewa ta yi tsarin da tauraron ɗan'adam na NIGCOMSAT yake samarwa zai taimaka wajen rage giɓin sadarwa tare da tallafa wa bunƙasar tattalin arzikin ƙirƙire-ƙirƙire da fasahar dijital.
Ta ce, "Wannan zai samar da sababbin damarmaki ga masu samar da abun ciki, gidajen watsa shirye-shirye, masana'antun cikin gida, masu saka hannun jari da masu samar da fasaha, tare da ƙarfafa matsayin Nijeriya a matsayin jagorar tsarin watsa shirye-shiryen dijital a Afrika."
Babban Baƙon na Musamman a taron, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Benjamin Okezie Kalu, ya bayyana ƙaddamar da DSO ɗin a matsayin wata babbar nasara ta ƙasa da ke nuna irin ƙarfin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki a masana'antu.
Ya ce, "Wannan shiri zai faɗaɗa damar samun ingantattun ayyukan watsa shirye-shirye, ya samar da ayyukan yi, ya ƙarfafa saka hannun jari tare da samar da sababbin damarmaki a ɓangarorin yaɗa labarai da masana'antar ƙirƙire-ƙirƙire."
A cewar sa, nasarar aiwatar da wannan manhaja tana nuna hangen nesan Shugaba Tinubu na sauyin fasahar zamani da bunƙasar tattalin arziki, tare da taimaka wa Nijeriya wajen gina tattalin arziki mai haɗin kai, mai gogayya da sauran ƙasashe kuma mai yalwar arziki.
Taron ya samu halartar Babbar Sakatariya ta Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem C. Ukaire; Babban Sakatare na Ma'aikatar Sadarwa, Ƙirƙire-ƙirƙire da Tattalin Arzikin Dijital, Injiniya Nadungu Gagare; Shugaban Ƙungiyar Masu Watsa Shirye-shirye ta Nijeriya (BON), Tony Akiotu; Darakta Janar na Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), Salihu Abdullahi Dembos; Darakta Janar na Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Baba Ndace; Darakta Janar na Gidan Rediyon Tarayya (FRCN), Mohammed Bulama; Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Lanre Issa-Onilu; Darakta Janar na Hukumar Kula da Talla ta Nijeriya (ARCON), Dakta Olalekan Olumuyiwa Fadolapo, tare da sauran manyan baƙi da masu ruwa da tsaki daga ɓangarorin sadarwa da watsa shirye-shirye.








No comments