Babban Bankin Nijeriya (CBN) ta fitar da sabbin ƙa’idojin bayar da lasisi da kuma kula da Kamfanonin Rukunin Harkokin Kuɗi (Financial Holdin...
Cikin wata takardar da CBN ya fitar tun a ranar 10 ga Yuni, 2026 mai lamba FPR/DIR/PUB/CIR/001/017, wadda Daraktar Sashen Manufofi da Tsare-tsaren Kuɗi, Dokta Rita Sike ta sanya wa hannu, tana ɗauke da taken “Daftarin Sabunta Ƙa’idojin Bayar da Lasisi da Kula da Kamfanonin 'Financial Holding Companies' a Nijeriya.”
Bayanan da ke ƙunshe a cikin wannan takarda na ɗauke da muhimman shawarwari kan ware ayyuka daban-daban (Ring-Fencing Operations), buƙatun jari, tsarin shugabanci da kuma tuntuɓar jama’a, domin ƙara tabbatar da zaman lafiyar ɓangaren bankuna da kare kuɗaɗen masu ajiya.
Sabbin ƙa’idojin sun tanadi cewa lallai dole 'HoldCos' su mallaki aƙalla kashi 51 cikin 100 na hannun jari a kowane reshe da ke ƙarƙashin su, tare da ƙarin buƙatun jari domin tabbatar da zaman lafiyar tsarin kuɗi.
Har ila yau, CBN na ci gaba da tabbatar da aiwatarwa da sa ido kan sabon kundin dokokin kasuwar canjin kuɗi domin ƙara gaskiya, faɗaɗa mahalarta kasuwa, tsaurara ƙa’idojin tattara bayanai da kuma ƙarfafa sa-ido a kasuwar EFEM.
An fitar da wannan bayani tare da bayyana ƙirƙiro shi a lokacin gagarumin taron karrama CBN da lambar yabon gwarzon manyan bankuna na shekara, wanda aka yi a Landan, cikin makon jiya.
Hakan wasu bayyananun alamomi ne da ke ƙara tabbatar da cewa ladar aiki tuƙuru da Olayemi Cardoso da tawagar sa suka yi shi ne ƙarin aiki, kuma alamu sun nuna cewa sun ƙudiri aniyar ci gaba da wannan tafiya domin cimma ƙarin nasarori, inji wasu masana harkokin kuɗi da suka bayyana ra'ayoyin su.

No comments