Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, murnar zagayowar ranar haihuwarsa, ...
A cikin saƙon taya murnar da ya fitar a ranar Juma'a, 19 ga Yuni, 2026, Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Sanata Barau ya kasance jagora mai hangen nesa, wanda ya yi fice wajen jagoranci da kuma samar da dokoki masu amfani da ke ƙarfafa adalci, ci gaba da haɗin kan ƙasa.
Shugaban Ƙasar ya ce Sanata Barau, wanda ke wakiltar Sanatoriyar Kano ta Arewa kuma yake riƙe da muƙamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa tare da zama Mataimakin Kakakin Majalisar ECOWAS na Farko, ya nuna ƙwarewa da nagarta tun daga fannin Akanta da ya karanta har zuwa aikin siyasa da dokoki.
"Sanata Barau Jibrin ya kasance mutum mai fice a duk inda ya tsinci kansa. Tun yana fannin Akanta ya nuna ƙwarewa ta musamman."
"A Majalisar Dokoki, ya dauki nauyin muhimman kudurori masu amfani ga ƙasa. Haka kuma ya kafa tarihi wajen shugabantar Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai da kuma na Majalisar Dattawa a lokuta daban-daban." Inji Tinubu
Shugaban Ƙasar ya tunatar da cewa al'ummar Tarauni ne suka fara ba Sanata Barau damar wakiltarsu a Majalisar Wakilai tun a shekarar 1999, duk da cewa asalinsa daga Kano ta Arewa yake. Ya bayyana cewa hakan ya samo asali ne daga yadda ya sadaukar da kansa wajen bunƙasa harkokin lafiya, ilimi da ci gaban al'umma.
Shugaba Tinubu ya kuma yabawa Sanatan, wanda aka fi sani da "Maliya", bisa irin hidimomin da ya yi wa Jihar Kano a matsayin Shugaban Kamfanin Zuba Jari da Kaddarori na Jihar Kano da kuma Kwamishinan Kimiyya da Fasaha.
A ƙarshe, Shugaban Ƙasa ya yi addu'ar Allah Ya ƙara wa Sanata Barau shekaru masu albarka, lafiya, hikima da ƙarfin guiwa domin ci gaba da hidimtawa Nijeriya da al'ummarta.

No comments