Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CBN Ya Umarci Bankuna Da Kamfanonin 'fintech' Su Bayyana Masu Hannayen Jarin Su, Su Adana Bayanai A Cikin Ƙasa

  Daga Ashafa Murnai Barkiya A wani sabon ƙoƙarin tsaftace hanyoyin hadahadar kuɗaɗen a zamanance, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci ba...


 
Daga Ashafa Murnai Barkiya

A wani sabon ƙoƙarin tsaftace hanyoyin hadahadar kuɗaɗen a zamanance, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umarci bankuna, kamfanonin fintech da sauran cibiyoyin kuɗi da ke gudanar da harkokin biyan kuɗi ta yanar gizo su, cewa su bayyana haƙiƙanin Masu Hannayen Jari na Ainihi (Ultimate Beneficial Ownership – UBO), a wani mataki na ƙarfafa gaskiya da riƙon amana a fannin hadahadar kuɗi.

CBN ya bayyana cewa umarnin na da nufin rage haɗarin mamayar kasuwa da wasu kamfanoni ke yi, ƙara bayyana gaskiyar masu kamfanonin da kuma ƙarfafa juriyar tsarin biyan kuɗi na Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin zuwa ga Bankunan Karɓar Ajiya (DMBs), Masu Ba da Sabis na Biyan Kuɗi (PSPs), kamfanonin fintech da sauran cibiyoyin hadahadar da yake sa ido a kan su, CBN ya ce saurin bunƙasar ayyukan biyan kuɗi ta zamani ya haifar da damuwa kan dogaro da wasu tsirarrun kamfanoni, rinjayen kasuwa da kuma rashin cikakken bayani kan waɗanda suka mallaki kamfanonin.

A cewar mai kula da harkokin, yawaitar amfani da ayyukan kuɗi na dijital da fitowar manyan kamfanoni masu rinjaye a muhimman ayyukan biyan kuɗi sun kuma ƙara jawo damuwa game da yadda ake adanawa da sarrafa muhimman bayanan biyan kuɗi da ake samarwa a cikin Nijeriya.

CBN ya umarci duk cibiyoyin da abin ya shafa su riƙa adana sahihan bayanan masu mallakar kamfanonin na ainihi (UBO) tare da sabunta su lokaci-lokaci, sannan su gabatar da bayanan idan mai kula da kuma sa-ido kan harkokin ya buƙata.

Wannan sanarwar ta kuma bayyana cewa duk bankuna, masu ba da sabis na biyan kuɗi da sauran cibiyoyin kuɗi masu gudanar da ayyukan biyan kuɗi a tsarin dijital dole ne su bi dokoki da ƙa’idojin da suka shafi yaƙi da halatta kuɗaɗen haram (AML), yaƙi da ɗaukar nauyin ta’addanci (CFT) da kuma hana yaɗuwar muggan makamai (CPF).

Kuma CBN ya kuma ƙaddamar da manufar adana bayanai a cikin ƙasa (Data Localisation Policy), wadda ta tanadi cewa duk bayanan mu’amalolin biyan kuɗi da aka samar a Nijeriya, to dole ne a adana su kuma a sarrafa su a cikin ƙasar, bisa tanadin dokokin kariyar bayanai da suka dace.

Ana sa ran fara aiwatar da wannan umarni daga ranar 1 ga Janairu, 2027.

Domin ƙarfafa gasa mai kyau da hana mamayar kasuwa fiye da kima, CBN ya kuma fitar da sabbin ƙa’idojin tsarin kasuwa ga harkokin bayar da katin biyan kuɗi wato 'card issuing' da karɓar biyan kuɗi daga ‘yan kasuwa, abin da a Turance aka fi sani da 'merchant acquiring'.

A ƙarƙashin sabon tsarin, duk wata cibiyar kuɗi da ke da fiye da kashi 25 cikin 100 na kasuwar bayar da kati a cikin watanni 12 masu jere, za a takaita ta zuwa iyakar kashi 15 cikin 100 kawai na kasuwar karɓar kuɗi daga 'yan kasuwa a wannan lokaci.

Haka kuma, cibiyar da ke da fiye da kashi 25 cikin 100 na kasuwar, ba za ta mallaki fiye da kashi 15 cikin 100 na kasuwar bayar da kati ba.

CBN ya kuma umarci cibiyoyin da yake sa ido a kan su da su riƙa gabatar da rahotannin rabon hadahadar kasuwa kowane wata, bisa tsarin bayanai da jadawalin da ya tanada.

Wanarwar ta jaddada cewa duk cibiyoyin kuɗi, ko suna aiki da kan su ko kuma a matsayin wani ɓangare na rukuni, dole ne su bi waɗannan sabbin ƙa’idoji kafin ranar 31 ga Disamba, 2026.

CBN ya yi gargaɗi cewa zai sanya ido sosai kan yadda ake bin umarnin, tare da ɗaukar matakan hukunci na sa ido kan duk wata cibiyar da ta gaza bin sabbin ƙa’idojin, bisa dokoki da ƙa’idoji.

No comments