Daga Zubairu Lawal, Lafia Wani jigo na jam’iyyar APC, Alhaji Isiaka Abdullahi, ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da jam...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Wani jigo na jam’iyyar APC, Alhaji Isiaka Abdullahi, ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da jami’an tsaro game da yadda suka gudanar da zaɓen cike gurbin kujerar Sanatan Nasarawa ta Arewa cikin lumana da tsari.
Da yake zantawa da manema labarai a rumfar zaɓe ta P018 da ke garin Nasarawa Eggon, a gundumar zaɓe ta Alizaga, Abdullahi ya ce an samu kyakkyawan tsari a rumfar zaɓen duk da wasu ƙananan matsaloli da na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS ta fuskanta da farko.
Ya bayyana cewa ya samu damar kaɗa ƙuri’arsa cikin nasara, tare da sauran masu zaɓe da dama da suka halarci zaɓen.
“Ya zuwa yanzu komai yana tafiya yadda ya kamata. INEC ta yi aiki mai kyau, jami’an zaɓe suna bakin aikinsu, kuma na’urar BVAS tana aiki bayan an gyara ƙananan matsalolin da ta samu a farko,” in ji shi.
Abdullahi ya ce yanayin zaɓen ya kasance cikin lumana, inda masu zaɓe ke ci gaba da zama a wuraren zaɓensu domin sa ido da kare ƙuri’unsu har zuwa lokacin ƙirga ƙuri’u.
Ya ƙara da cewa jama’a suna farin ciki da damar da suka samu na zaɓar shugabannin da za su wakilce su tare da kawo ribar dimokuraɗiyya ga al’ummarsu.
Jigon na APC ya kuma yaba wa jami’an tsaro, kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaki kan gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da sahihin zaɓe.
Ya bayyana fatan cewa zaɓen zai gudana cikin nasara tare da samar da sakamakon da zai nuna ra’ayin mafi rinjayen masu zaɓe.
“Mutane suna cikin kwanciyar hankali da lumana. Muna sa ran kyakkyawan sakamako saboda shirye-shiryen da aka yi da haɗin kan duk masu ruwa da tsaki,” in ji shi.
Zaɓen cike gurbin kujerar Sanatan Nasarawa ta Arewa na gudana ne a sassa daban-daban na mazaɓar domin zaɓar sabon wakili a Majalisar Dattawan Najeriya.

No comments