Gwamnatin Tarayya ta ƙarƙashin Asusun Bunƙasa Noma na Ƙasa (NADF) ta ƙaddamar da kashi na farko na Shirin Tallafin Kayan Aikin Noma (FISP) a...
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da shirin a jihar Katsina, Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, CON, ya bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na bunƙasa samar da abinci da kuma haɓaka tattalin arzikin karkara, daidai da manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.
Ministan ya bayyana cewa kowace daga cikin jihohin biyar da suka ci gajiyar shirin ta samu buhunan taki 20,160, waɗanda za a raba wa manoma 5,040 da aka yi wa rijista tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar Manoma ta Ƙasa (AFAN).
A cewarsa, manufar shirin ita ce rage gibin da ke tsakanin ƙananan manoma da manyan manoma ta fuskar yawan amfanin gona, tare da tallafa wa masana’antun taki na cikin gida domin ƙara yawan samar da taki, samar da ayyukan yi da kuma ƙarfafa tsarin samar da abinci a ƙasar nan.
Sanata Kyari ya tunatar da cewa a baya gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin AgGrow-1, wanda ya haɗa masu sarrafa kayan amfanin gona da manoma da aka yi wa rijista domin tabbatar da samun kasuwa ga amfanin gonarsu da kuma inganta darajar noma.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi samar da wadataccen abinci, waɗanda ke taimakawa wajen daidaita farashin kayan abinci, rage matsin hauhawar farashi da kuma ƙarfafa sauye-sauyen tattalin arzikin noma a Najeriya.
“Ba a samun nasarar samar da wadataccen abinci a rana ɗaya. Ana samun ta ne a kowace kaka, ta hanyar kowane manomi da kuma kowane kayan tallafin noma da aka samar. Yau yankin Arewa maso Yamma ne ya samu wannan dama,” in ji Ministan.
Shirin na FISP na daga cikin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka domin ƙara yawan amfanin gona da tabbatar da wadatar abinci a faɗin ƙasar nan.

No comments