Bayan shafe sama da shekaru 30 ana fama da matsananciyar zaizayar ƙasa da lalacewar muhalli a Rigasa da wasu yankuna na Ƙananan Hukumomin Ka...
Bayan shafe sama da shekaru 30 ana fama da matsananciyar zaizayar ƙasa da lalacewar muhalli a Rigasa da wasu yankuna na Ƙananan Hukumomin Kaduna ta Kudu da Igabi, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ware naira biliyan 34 da nufin kawo ƙarshen matsalar tare da farfaɗo da yankunan da abin ya shafa.Shirin, wanda Ma’aikatar Muhalli da Albarkatun Ƙasa ta jihar za ta aiwatar, zai shafi wani yanki mai tsawon kilomita 17, tare da manufar dawo da gonaki da filayen da suka lalace, daƙile ci gaba da zaizayar ƙasa, kare rayuka da dukiyoyi, da kuma inganta rayuwar al’ummomin da abin ya shafa.
Bayan duba wuraren da matsalar ta fi kamari, Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa zaizayar ƙasar ta jima tana haddasa asarar rayuka, lalata gidaje da dukiyoyi, tare da jefa dubban iyalai cikin halin ƙunci.
Ya ce wannan aiki ba wai aikin muhalli kaɗai ba ne, illa wata babbar hanyar bunƙasa rayuwar al’umma, kare rayuka, samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da cewa jama’a suna rayuwa cikin aminci da walwala.
Gwamnan ya bayyana cewa an riga an samar da kudaden da za a gudanar da aikin, inda ake sa ran fara aikin cikin makonni biyu masu zuwa, tare da kammala shi cikin watanni 18.
Ya kuma bayyana cewa duk da gidaje sama da 1,200 za su iya fuskantar tasirin aikin, gwamnatin jihar ta ware sama da naira biliyan 2 domin biyan diyya da tallafawa wadanda za abin ya shafa.
A cewarsa, wannan jarin naira biliyan 34 wata shaida ce ta kudurin gwamnatinsa na magance matsalolin da aka daɗe ana watsi da su, musamman wadanda suka shafi rayuwa da jin dadin jama'a.
Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa aikin zai samar da guraben ayyukan yi, bunƙasa harkokin kasuwanci da tattalin arziki, tare da anfani kai tsaye ga sama da mutane miliyan biyu da ke zaune ko gudanar da harkokin su a yankunan da abin ya shafa.
Ya ce: “Tsawon shekaru, zaizayar ƙasa ce ke tsara makomar waɗannan al’ummomi. Yau muna sauya wannan labari. Muna dawo da ƙasa mai amfani, muna farfaɗo da rayuwar jama'a, muna kare rayuka tare da gina makoma mai kyau ga sama da mutane miliyan biyu.”
Mazauna yankunan da abin ya shafa sun bayyana farin cikinsu kan wannan mataki, suna masu cewa wannan ne karo na farko da suka ga wani shiri mai girman da zai iya kawo ƙarshen matsalar da ta addabe su kusan shekaru talatin.
Daya daga cikin shugabannin al’umma, Yusuf Wada Muhammad, ya ce matsalar zaizayar ƙasar ta janyo asarar rayuka da dukiyoyi na miliyoyin naira, tare da lalata gidaje da gonaki da dama.
Ya ce ziyarar da gwamnan ya kai yankin da kuma ƙaddamar da wannan shiri sun sake dawo da fata da ƙwarin gwiwa ga al’ummomin yankin cewa matsalar da suka daɗe suna fama da ita za ta zama tarihi.


No comments