Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a N...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Nijeriya.
A sashe na jawabin sa na Ranar Dimokuraɗiyya, shugaban ya bayyana cewa gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci a bangaren tsaro tare da amincewa da ɗaukar sabbin jami'an 'yan sanda sama da 50,000 da kuma dubban sababbin sojoji.
Ya ce kasafin kuɗin shekarar 2026 ya ware Naira tiriliyan 5.41 domin tsaro, wanda shi ne mafi girma da aka taba warewa wannan bangare a tarihin ƙasar.
Tinubu ya ce sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a yaƙi da ta'addanci, inda ya bayyana cewa an lalata wani babban sansanin kungiyar ISWAP a yankin Arege na Jihar Borno.
A cewarsa, yawan mutanen da ake kashewa sakamakon ta'addanci ya ragu da kashi 81 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar 2015, yayin da sama da 'yan ta'adda 13,000 suka mutu a cikin shekara guda.
Sai dai shugaban ya ce har yanzu gwamnati tana bai wa masu son mika wuya dama ta hanyar shirin Operation Safe Corridor, inda ya ce sama da mutane 124,000 daga cikin mayaƙa da iyalansu suka ajiye makamansu tun daga shekarar 2023.
Ya kuma gargadi 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta'addanci da su mika wuya ko kuma su fuskanci cikakken ƙarfin gwamnatin Najeriya.

No comments