Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

DIMOKURAƊIYYA A SHEKARU 27: Tinubu Ya Yaba Wa Jaruman 12 ga Yuni

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su ci gaba da kare dimokuraɗiyya tare da ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, yana...


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su ci gaba da kare dimokuraɗiyya tare da ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, yana mai cewa ƙasar ta samu mafi tsawon lokacin mulkin farar hula a tarihinta.

A jawabin da ya gabatar domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni, Shugaba Tinubu ya ce shekaru 27 da suka gabata sun nuna cewa Najeriya na iya gudanar da sauye-sauyen mulki cikin lumana ta hanyar zaɓe da bin doka.

Ya kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), jami'an tsaro da jam'iyyun siyasa da su tabbatar da cewa zaɓukan da za a gudanar a jihohin Ekiti da Osun sun kasance cikin gaskiya da adalci.

Shugaban ya yabawa Majalisar Tarayya, bangaren shari'a, kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyin farar hula bisa rawar da suke takawa wajen kare dimokuraɗiyyar ƙasar.

Tinubu ya kuma yi amfani da damar wajen tunawa da marigayi MKO Abiola, Kudirat Abiola, Shehu Musa Yar'Adua, Gani Fawehinmi da sauran fitattun mutane da suka taka rawa a gwagwarmayar dawo da mulkin dimokuraɗiyya.

Haka kuma ya sanar da cewa gwamnatin tarayya za ta sauya sunan Cibiyar Nazarin Man Fetur da ke Kaduna zuwa Jami'ar Kimiyyar Ƙasa da Fasahar Injiniya ta Janar Shehu Musa Yar'Adua domin girmama gudummawar marigayin.

Shugaban ya kuma bayyana sunayen wasu fitattun 'yan gwagwarmayar dimokuraɗiyya da sojojin da suka mara wa gwagwarmayar baya waɗanda za a karrama da lambobin yabo na ƙasa.
 

No comments