Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Shugaba Tinubu, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya yi Ƙarin Haske Kan Ɗaukar Masu Tsaro...
Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai ga Shugaba Tinubu, Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya yi Ƙarin Haske Kan Ɗaukar Masu Tsaron Daji 1,000 a Jihar Oyo.Tun jiya da jaridu suka fara bada labarin aniyar ɗaukar masu tsaron daji (Forest Guards) guda 1,000 a jihar Oyo sakamakon kidnapping da aka yi kwanaki na lura wasu mutanen mu na Arewa a Social Media suna ƙorafi ko shaguɓen cewa "an taɓa 'yan gata". A ganin su wannan abu ne kawai za a yi domin Yarabawa saboda matsalar tsaro ta shafe su. To ba haka ba ne.
A yanzu haka akwai jihohi 10 da aka kafa rundunar Forest Guards da kuma jihohin da za a kafa, duk a Arewa. Kuma kowanne an ɗauki mutum kimanin 1,000 ɗin ne.
Jihohin da suke da Forest Guards:
1. Borno
2. Yobe
3. Adamawa
4. Kwara
5. Sokoto
6. Kebbi
7. Niger
8. Plateau
9. Benue
Wanda suke kan hanya
1. Kaduna
2. Edo
3. Kogi
4. Bauchi







No comments