Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CBN Ya Ƙara Wa’adin Cika Ƙa'idoji Da Nisan Zangon Amfani Da PoS

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara wa’adin fara aiwatar da tsarin tantance wurin aiki wanda a Turance ake kira 'geo-fencing' na na...

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara wa’adin fara aiwatar da tsarin tantance wurin aiki wanda a Turance ake kira 'geo-fencing' na na’urorin PoS zuwa ranar 1 ga Agusta, 2026.

Wannan dai ya ƙunshi ƙara wa'adin cika ƙa'idoji da sharuɗɗan da CBN ya gindiya, tare kuma da ƙara faɗin nisan zangon da za a iya aiki da kowane PoS a faɗin Nijeriya.

CBN ya yi haka ne domin bai wa cibiyoyin kuɗi da masu samar da ayyukan biyan kuɗi ƙarin lokaci su cika sabon sharaɗin doka da aka kafa domin ƙarfafa sa-ido kan hanyoyin biyan kuɗi na zamani.

An bayyana wannan umarni ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 29 ga Mayu, 2026, wato a ranar Juma’ar da ta gabata, wadda Daraktar Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi ta CBN, Rakiya Mohammed, ce ta sanya hannu a kan sanarwar.

An aika da sanarwar ne zuwa Bankunan Kasuwanci (DMBs), Bankunan Microfinance, Masu Gudanar da Hadahadar Kuɗi ta Kafafen Sadarwar Zamani (Mobile Money Operators), Kamfanonin Canjawa da Sarrafa Ma’amaloli, Masu Samar da Sabis na Na’urorin Biyan Kuɗi, Masu Samar da Hanyoyin Biyan Kuɗi, Super Agents da sauran masu lasisi a tsarin biyan kuɗi na Nijeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa an sake duba jadawalin aiwatar da manufar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma la’akari da ƙalubalen da suka taso wajen aiwatar da wata sanarwa da aka fitar a ranar 25 ga Agusta, 2025, wadda ta shafi sauyawa zuwa tsarin saƙonnin biyan kuɗi na ISO 20022 da kuma wajabta sanya bayanan wurin aiki ga dukkan na’urorin biyan kuɗi.

Idan ba a manta ba, tun a watan Agustan 2025 ne dai CBN ya umarci cewa dukkan na’urorin PoS a faɗin ƙasar nan su kasance an tantace nisan wuraren da za a iya amfani da su, cikin kwanaki 60, a matsayin wani mataki na rage damfara da ƙarfafa sa-ido kan harkokin biyan kuɗi na zamani.

A cikin sabon umarnin, CBN ya sanar da manyan sauye-sauye guda biyu.
Na farko, ya ƙara iyakar nisan da aka amince da domin amfani da kowace na’urar PoS daga mita 10 zuwa mita 70.

Sai na biyu kuma CBN ya ɗage ranar da za a fara tilasta bin dokar ta 'geo-fencing' zuwa ranar 1 ga Agusta, 2026.

Sanarwar ta ce:
“An ƙara iyakar nisan amfani da PoS daga mita 10 zuwa mita 70.”
Ta kuma ƙara da cewa:
“An tsawaita lokacin fara aiwatar da tsarin nisan amfani da na’urorin PoS zuwa ranar 1 ga Agusta, 2026.”

Tsarin 'geo-fencing' yana nufin cewa na’urar PoS za ta yi aiki ne kawai a wurin da aka amince, kuma aka danganta shi da ɗan kasuwa ko wakilin da ke amfani PoS ɗin.

An tsara wannan mataki ne domin inganta sa-ido kan ma’amaloli, rage amfani da hanyoyin biyan kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ƙarfafa sahihanci da tsaron tsarin biyan kuɗi na ƙasa.

CBN ya umurci dukkan cibiyoyin da abin ya shafa da su gabatar da hujjar cewa sun cika waɗannan ka’idoji kafin sabon wa’adin da aka sanya.
 

Sanarwar ta ce:
“Dole ne a aika da hujjar bin waɗannan umarni zuwa ga Daraktan Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi ta hanyar adireshin imel paymentdata@cbn.gov.ng kafin ranar 31 ga Yuli, 2026.”
 

Har ila yau, darakta mai kula da harkokin ta umurci cibiyoyin kuɗi da su warware duk wata matsalar fasaha ko ta gudanarwa da suke fama da su, domin sauƙaƙa aiwatar da wannan manufa.

Sanarwar ta ce:
“Ana buƙatar cibiyoyin kuɗi su magance dukkan matsalolin gudanarwa da suke da su cikin wa’adin da aka gindaya domin sauƙaƙa bin dokar.”

Ana sa ran wannan ƙarin wa’adi zai bai wa masu gudanar da ayyukan biyan kuɗi damar kammala inganta tsarin su, daidaita wuraren da na’urorin PoS suke aiki da sabbin ƙa’idojin CBN, tare da magance sauran matsalolin gudanarwa kafin fara aiwatar da dokar a watan Agusta.
 

No comments