Wata matar aure mai shekara 28 mai suna Firdausi Musa tare da ’ya’yanta biyu ƙanana sun samu munanan ƙuna, a yayin da ake zargin kishiyarta,...
Wata matar aure mai shekara 28 mai suna Firdausi Musa tare da ’ya’yanta biyu ƙanana sun samu munanan ƙuna, a yayin da ake zargin kishiyarta, Maryam Muhammad, ta zuba musu fetur tare da banka musu wuta a unguwar Hotoro da ke Jihar Kano.
Faruwar wannan lamari a daren Litinin a yankin Mai Allo da ke unguwar Hotoro, ya jefa mazauna yankin cikin firgici, yayin da ake tsare da wacce ake zargin a ofishin ’yan sanda na Mariri.
Ƙananan yaran da suka ƙone sun haɗa da Khadija Ya’u mai shekara 7 da Isma’il Ya’u mai shekara 3, kuma suna karɓar magani tare da mahaifiyarsu a Asibitin Ƙashi na Ƙasa da ke Dala da kuma Asibitin Ƙwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Shi ma mijinsu kuma, Malam Saminu, wanda shi ma ya samu ƙonewa yayin da yake ƙoƙarin ceton su daga wutar, yana ci gaba da karɓar magani.
Wani ƙanin Firdausi mai suna Buhari Musa Sa’ad, ya shaida wa wakilinmu, ce sun samu kiran gaggawa ne da misalin ƙarfe qarfe 3 cewa kishiyar ’yar uwarsa ta banka mata wuta da mijinta da kuma yaran biyu.
“An kira mu cikin dare aka sanar da mu cewa kishiyar ce ta ƙona ’yar uwata da mijinta da yaran biyu,” in ji shi.
A cewarsa, Firdausi ba ta yi ko makonni biyu da tarewa a gidan mijin nata ba kafin faruwar lamarin.
Ya ƙara da cewa, “Yaran da suka qone ’ya’yanta ne daga aurenta na baya. Ba ’ya’yan mijin ba ne, wanda yake aikin tuƙa baburin A-Daidaita-Sahu.”
Ya bayyana cewa an fara kai waxanda suka jikkata Asibitin Ƙwararru na Sir Sunusi, kafin daga baya a mayar da su Asibitin Ƙwararru na Murtala sannan daga bisani aka mayar da su Asibitin Ƙashi na Ƙasa da ke Dala saboda tsananin ƙonewar da suka yi.
“Shi ma mijin ya samu ƙonewa a ƙafafunsa yayin da yake ƙoƙarin ceton yaran,” in ji shi.
Wata ’yar uwar Firdausi mai suna Ruƙayya, ta shaida wa wakilinmu cewa tun kafin harin, Firdausi ta riƙa ƙorafin cewa kishiyarta na yi mata barazana da tsoratarwa.
“Muna zaune a nan lokacin da aka kawo ta, kuma da bakinta ta gaya mana cewa kishiyarta ce ta zuba mata fetur sannan ta ƙyasta ashana,” in ji Ruƙayya.
Ta bayyana cewa tun da farko a ranar, sai da Firdausi ta bar gidan saboda yawan barazanar da kishiyar take mata, amma daga baya ta dawo bayan mijinta ya shiga tsakani.
“Har da taɓarya uwar gidan ta taɓa bin ta, amma ta tsere. Daga baya mijinta ya sasanta su sannan ya lallashe ta ta dawo gida. Abin takaici, cikin dare kishiyar ta zuba mata da yaran fetur sannan ta banka musu wuta,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa mijin ya samu damar ceto ɗaya daga cikin yaran kafin ya sake komawa domin ceton ƙaramin yaron, inda shi ma ya samu ƙonewa.
“Wutar ta ƙara ƙamari bayan kishiyar ta sake qyasta wata ashana, amma duk da haɗarin hakan, mijin ya sake shiga ya ceto ƙaramin yaron, inda a nan ne ya samu ƙonewa a ƙafafunsa,” in ji Ruƙayya.
Ta kuma bayyana cewa yaran marayu ne daga auren Firdausi na baya, kuma tun farko ’yan uwanta sun shawarce ta da kada ta sake aure, ta zauna ta mayar da hankali wajen kula da su.
“Ta yi aure ne a watan Ramadan, amma kusan makonni biyu ke nan kacal da tarewarta gaba ɗaya a gidan,” in ji ta.
Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano bai yi nasara ba zuwa lokacin haxa wannan rahoto.
.jpg)
No comments