Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kaduna Ta Shirya Tunkarar Ambaliya, Ta Ƙaddamar Da Gangamin Wayar Da Kai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma da kuma shirye-shiryen gaggawa domin daƙile illar ambaliyar ruwa bayan hasas...


Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma da kuma shirye-shiryen gaggawa domin daƙile illar ambaliyar ruwa bayan hasashen yanayi na shekarar 2026 da Hukumar Kula da Yanayi ta Ƙasa, (NiMet) ta fitar, wanda ya nuna cewa jihar Kaduna na daga cikin jihohin da ke cikin haɗarin ambaliya sakamakon yawan ruwan sama da ake sa ran za a samu a bana.

A wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa tana ƙara ɗaukar matakan kariya domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma ta hanyar wayar da kai da kuma hada kai tsakanin hukumomin bayar da agajin gaggawa.

Sanarwar ta ce ana sa ran damina za ta fara tsakanin ranar 19 ga watan Mayu zuwa 10 ga watan Yuni na shekarar 2026, yayin da ake sa ran za ta ƙare tsakanin ranar 5 zuwa 21 ga watan Oktoba.

Har ila yau, hasashen ya nuna yiwuwar samun kwanaki 21 na fari tsakanin watan Yuni da Agusta, lamarin da ka iya ƙara haddasa matsalolin ambaliya da sauran ƙalubalen muhalli.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar tana ɗaukar wannan hasashe da muhimmanci, yana mai jaddada cewa shiri tun da wuri da haɗin kan jama’a na da matuƙar muhimmanci wajen rage illar ambaliya a cikin al’umma.

Maiyaki, ya ƙara da cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu tare da haɗin gwiwar Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna,  (KADSEMA), sun fara gangamin wayar da kai a faɗin jihar domin ilmantar da jama’a hanyoyin kariya daga ambaliya da matakan kare kai.

Gwamnatin ta kuma buƙaci mazauna jihar da su rika tsaftace magudanan ruwa da ke kusa da gidaje da wuraren kasuwanci, su guji zubar da shara a hanyoyin ruwa, tare da amfani da buhunan yashi da sauran hanyoyin kariya daga ambaliya.

Haka kuma, gwamnatin ta yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addini, kafafen yada labarai da ƙungiyoyin fararen hula da su mara wa ƙoƙarin gwamnati baya ta hanyar wayar da kai da yada sahihan bayanai ga jama’a.

A wani bangare na matakan gaggawa, hukumar KADSEMA ta fara tantance yankunan da ke cikin haɗarin ambaliya, tare da ƙara ƙarfafa tsarin bayar da agajin gaggawa da kuma shirya kayan ceto a yankunan da ke cikin haɗari.

Kwamishinan ya tabbatar da cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma na ci gaba da kasancewa babban abin da gwamnatin jihar Kaduna ta sa a gaba yayin daminar bana.
 

No comments