Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sanata Tambuwal Ya Janye Takarar Sa Ga Faruk Malami Yabo

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, ...


Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya janye daga takarar kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, tare da miƙa tikitin ga tsohon Kwamishinan Kuɗi na jihar, Faruk Malami-Yabo.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa Tambuwal, wanda ake kallon jagoran ADC a jihar Sokoto, ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da haɗin kai a cikin jam’iyyar bayan tattaunawa da sabanin ra’ayi da suka taso kan zaben ‘yan takara gabanin babban zaben 2027.

Da  ya ke tabbatar da lamarin a wata hira ta wayar tarho da wakilin Punch a ranar Juma’a, Sakataren Yaɗa Labarai na ADC a jihar Sokoto, Lamir Aminu, ya ce Tambuwal ya sadaukar da burinsa ne saboda zaman lafiya da daidaito a cikin jam’iyyar.

Ya ce, “Sanata Tambuwal ya yanke shawarar hakura da tikitin domin ƙarfafa haɗin kai da kuma dimokuraɗiyya ta cikin gida a jam’iyyar.”

Ya kara da cewa yawancin tikitin takarar kujerun Majalisar Wakilai ta tarayya a jihar ma an bai wa matasa ‘yan takara.

Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da ake ci gaba da sauya sheka da sabbin tsare-tsaren siyasa a cikin ADC a jihar Sokoto kafin babban zaben 2027 da aka shirya gudanarwa ranar 20 ga watan Fabrairu, 2027.
 

No comments