Wani mazaunin garin Zariya mai suna Ahmad Sa’idu, wanda aka fi sani da Abba, ya bayyana dalilin da ya sa ya riƙe rigar Kakakin Majalisar Wak...
Wani mazaunin garin Zariya mai suna Ahmad Sa’idu, wanda aka fi sani da Abba, ya bayyana dalilin da ya sa ya riƙe rigar Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Abbas Tajudeen, yayin wani taron siyasa da aka gudanar a birnin.
Ahmad Sa’idu ya yi wannan bayani ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin a Zariya, inda ya kuma nemi afuwar Kakakin Majalisar kan lamarin da ya faru a lokacin taron bayyana aniyar Abbas Tajuddeen na sake tsayawa takara, wanda aka gudanar a filin Idi na Mallawa.
Ya ce abin da ya sa ya aikata hakan shi ne matsanancin halin da yake ciki sakamakon wata tsohuwar matsalar lafiya da ta shafi hannunsa na dama, wanda ya ce ya samu mummunan karaya a wani hatsari.
A cewarsa, hannun ya karye har sau uku, kuma har yanzu yana fama da matsanancin ciwo.
Sa’idu ya bayyana cewa ya fara jinya a Cibiyar Gyaran Ƙashi ta Gargajiya da ke Likoro, sannan daga bisani aka kai shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Ya ƙara da cewa, daga baya an tura shi Asibitin Sojoji na 44 da ke Kaduna domin ci gaba da kulawa.
Sai dai ya ce matsin tattalin arziƙi ya hana shi ci gaba da jinya bayan wasu da suka taimaka masa a baya sun daina bayar da gudunmawa.
A cewarsa, rashin kuɗin biyan kuɗaɗen asibiti ne ya tilasta masa neman wata hanya ta daban domin samun taimako.
Ya ce ya halarci taron ne bayan da ya samu labarin cewa Kakakin Majalisar zai kasance a wurin, domin ya samu damar gabatar masa da halin da yake ciki kai tsaye.
“Ni ɗaya ne daga cikin magoya bayan Kakakin Majalisar. Na je wurin ne domin neman taimakonsa.
Da na kusance shi, sai na riƙe rigarsa ina ƙoƙarin nuna masa hannuna da ya ji rauni, amma jami’an tsaro suka fizge ni daga wurin,” inji shi.
Ya nuna nadama kan yadda lamarin ya ɗauki hankalin jama’a, yana mai cewa bai taɓa nufin kunyata Kakakin Majalisar ba.
Ya ce da ace ya san abin zai janyo ce-ce-ku-ce sosai, da ya zaɓi ya ci gaba da jure radadin ciwon maimakon ya jefa mutumin da yake girmamawa cikin wani yanayi na rashin jin daɗi.
Sa’idu ya kuma yabawa Abbas Tajudeen bisa irin taimako da agajin da yake bai wa jama’a, yana mai cewa hakan ne ya ƙarfafa masa guiwar neman taimako kai tsaye daga gare shi.
Shi ma mahaifin Ahmad Sa’idu, Malam Sa’idu Ibrahim Abubakar, ya nemi afuwar Kakakin Majalisar, tare da zargin cewa wasu abokan hamayya na siyasa sun yi amfani da lamarin wajen yaɗa bayanan da ba su dace ba.
Ya ce iyalinsu sun shafe sama da shekaru biyu suna ƙoƙarin tara kuɗin jinyar ɗansa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da kuma Asibitin Sojoji na 44, amma daga bisani suka gaza ɗaukar nauyin kuɗaɗen.
Duk da abin da ya faru, mahaifin ya yabawa Abbas Tajudeen bisa amincewarsa da ɗaukar nauyin kuɗin jinyar ɗansa.
Ya bayyana wannan mataki a matsayin nuna tausayi da kulawa, tare da yi masa addu’ar samun nasara da ɗorewar shugabanci.

No comments