Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da tallata damarmakin tatt...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da tallata damarmakin tattalin arziki, al’adu da yawon buɗe ido na Nijeriya ga duniya, ta hanyar wani kundin bayanai na ƙasa da zai tattara bayanai kan damarmaki da ake da su a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Idris ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin da yake karɓar baƙuncin wata tawaga daga Hukumar Kula da Aikin Jarida ta Nijeriya (NPC), ƙarƙashin jagorancin Babban Sakataren hukumar, Dakta Dili Ezughah, gabanin ƙaddamar da kundin bayanan da aka shirya yi a ranar 17 ga Yuni, 2026.
Ministan ya yaba wa hukumar da abokan hulɗar ta bisa wannan shiri, wanda ya bayyana a matsayin muhimmin aiki na ƙasa da ke da nufin inganta martabar Nijeriya a idon duniya.
Ya ce: “Wannan aiki yana da muhimmanci saboda yana bayyana ɗimbin damar tattalin arziki da yawon buɗe ido da ƙasar mu take da su, a lokacin da wasu ke mayar da hankali kan munanan labarai game da Nijeriya. Abin da kuke yi yana taimakawa wajen nuna waɗannan damarmaki da ke faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya,” inji Ministan.
Idris ya ce shirin ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, musamman a ƙoƙarin da gwamnati ke yi na bunƙasa tattalin arziki ta hanyar yawon buɗe ido, al’adu da faɗaɗa ɓangaren da ba na mai ba.
Ya ce: “Ba mai kaɗai aka san Nijeriya da shi ba; an sanin mu da ɗimbin al’adun mu, wuraren yawon buɗe ido da damarmaki da ke faɗin ƙasar nan. Shugaba Tinubu ya fahimci muhimmancin al’adu da yawon buɗe ido wajen cigaban ƙasa, shi ya sa wannan gwamnati take ba wannan ɓangare kulawa ta musamman.”
Ya kuma yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin Hukumar Kula da Aikin Jarida ta Nijeriya da Hukumar Bunƙasa Yawon Buɗe Ido ta Nijeriya da Ma’aikatar Fasaha, Al’adu da Tattalin Arzikin Ƙirƙire-ƙirƙire da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya ce: “Shugaban Ƙasa yana faɗaɗa tubalin tattalin arzikin Nijeriya fiye da dogaro da mai, kuma yadda ƙasashen duniya suke ƙara nuna sha’awa ga ɓangaren tattalin arzikin mu da ba na mai ba alama ce cewa Ajandar Sabunta Fata tana haifar da sakamako mai kyau. Irin wannan kundin bayanai yana da muhimmanci saboda yana bai wa masu zuba jari da ƙasashen duniya sahihan bayanai kan ƙarfin tattalin arzikin Nijeriya da damarmakinta."
Ministan ya tabbatar wa da tawagar cewa ma’aikatar sa za ta ba da cikakken goyon baya domin samun nasarar ƙaddamar da kundin, tare da yaba wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, bisa goyon bayan da yake bai wa shirin.
Ya ce: “A shirye Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take domin tallafa wa wannan shiri na ƙasa saboda zai taimaka wajen inganta martabar Nijeriya a idon duniya. Muna kuma yaba wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bisa kulawar da yake bai wa wannan shiri.”
Tun da farko, Babban Sakataren Hukumar Kula da Aikin Jarida ta Nijeriya, Dakta Dili Ezughah, ya ce an ƙirƙiro shirin ne domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati wajen bayyana Nijeriya ta fuska mai kyau ga duniya.
Ya ce: “An ƙirƙiro wannan shiri ne domin haɗa ƙarfi da ƙarfe tsakanin hukumomin gwamnati wajen bayyana Nijeriya ta fuska mai kyau, kuma muna farin ciki da yadda Mataimakin Shugaban Ƙasa ya amince da shi a matsayin shiri na ƙasa. Mun samu gagarumin cigaba kuma yanzu muna matakin ƙarshe kafin ƙaddamar da shi."
Shi ma babban mai ba da shawara kan shirin, Mista Tajudeen Toyin-Oke, ya ce kundin bayanan ya ƙunshi cikakkun bayanai kan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, ciki har da damarmakin zuba jari, wuraren yawon buɗe ido, albarkatun ƙasa da ababen more rayuwa.
“An tsara kundin ne domin ya zama wata muhimmiyar madogara ta duniya ga duk wanda ke neman sahihan bayanai game da Nijeriya,” inji shi.
A nasa jawabin, Darakta-Janar na Hukumar Bunƙasa Yawon Buɗe Ido ta Nijeriya, Dakta Ola Awakan, ya ce shirin zai taimaka wajen inganta al’adu da wuraren yawon buɗe ido na Nijeriya a idon duniya.
Ya ce: “Nijeriya ƙasa ce mai ɗimbin labarai da damarmakin yawon buɗe ido, kuma wannan shiri zai taimaka wajen sauya munanan ra’ayoyi game da ƙasar mu tare da bayyana ƙarfin mu ga duniya.”

No comments