Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sai Tubabbun ’Yan Boko Haram Sun Yi Rantsuwa Da Alƙur’ani Suke Komawa Cikin Al’umma, In Ji Gwamnatin Borno

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa duk wasu tsofaffin ’yan ta’addan da ke shiga shirin gyaran hali da sake mayar da su cikin al’umma ana ...




Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa duk wasu tsofaffin ’yan ta’addan da ke shiga shirin gyaran hali da sake mayar da su cikin al’umma ana sanya musu rantsuwa da Alƙur’ani mai girma kafin a sallame su, domin tabbatar da cewa ba za su koma ayyukan tada ƙayar baya ba.

Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci Gaban Al’umma ta jihar Borno, Zuwaira Gambo, ce ta bayyana hakan yayin wata hira da ta yi da tashar talabijin ta News Central Television a ranar Litinin.

Ta bayyana cewa ana ɗaukar rantsuwar da Alƙur’ani a matsayin mataki na ƙarshe a tsarin gwamnatin Borno na kawar da tsattsauran ra’ayi da sake haɗa tsofaffin mayaƙa cikin al’umma.

A cewarta, “Da zarar sun bi dukkan matakan tsarin gwamnatin Borno, abu na ƙarshe shi ne su yi rantsuwa da Alƙur’ani. Kuma idan mutum ya rantse da Alƙur’ani, ya san girman abin da hakan ke nufi.”

Kwamishinar ta amince cewa har yanzu akwai ’yan Najeriya da dama da ke nuna shakku kan wannan shiri, musamman saboda tsoron cewa wasu daga cikin tsofaffin mayaƙan na iya komawa daji bayan an sake su cikin al’umma.

Sai dai ta ce ana yawan wuce gona da iri wajen irin waɗannan fargaba.

“Mutane na tunanin za su iya komawa daji; to ko sun koma ma, mutuwa ce za ta tarbe su. Saboda haka ba batun ko an yarda da su bane ko a’a. Dokar daji ita ce za ta yi hukunci kansu,” in ji ta.

Haka kuma ta bayyana ƙarancin kuɗaɗe a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar shirin, tana mai cewa gwamnati na ɗaukar nauyin abinci, sutura, ilimi da sauran buƙatun dubban mutanen da ke cikin shirin gyaran hali.

Shi ma yayin hirar, Mai Bai Wa Gwamna Babagana Zulum Shawara Kan Harkokin Tsaro, Abdullahi Ishaq, ya bayyana cewa sama da mutum 300,000 da suka haɗa da manoma, mata da yara ne suka miƙa wuya tun bayan fara rikicin ta’addanci a yankin.

Ya ƙara da cewa mutum 8,950 ne aka riga aka gyara tare da sake mayar da su cikin al’umma a rukuni takwas daban-daban ƙarƙashin shirin gwamnatin jihar.

A cewarsa, wannan shiri na gyaran hali na daga cikin manyan matakan da ake ɗauka domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar bayan shekaru na rikicin Boko Haram.

Rahoton ya kuma tuna cewa a watan Fabrairun 2026, tsofaffin ’yan ta’adda 117 ne suka kammala shirin gwamnatin tarayya na kawar da tsattsauran ra’ayi da sake haɗa mayaƙa cikin al’umma ƙarƙashin shirin Operation Safe Corridor a jihar Borno.

An gudanar da shirin gyaran nasu ne a sansanin Malam Sidi.

No comments