Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SHAWARAR CBN GA GWAMNATOCIN JIHOHI: "A Kiyaye Bin Ƙa'idojin Kashe Kuɗaɗe, A Daina Ciwo Bashin-alaƙaƙai "

Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin kashe kuɗi da kula da harkokin kuɗi daga gwamnatocin jihohi, domin tabbat...


Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin kashe kuɗi da kula da harkokin kuɗi daga gwamnatocin jihohi, domin tabbatar da nasarar sauya tsarin manufofin kuɗi zuwa tsarin da zai yi tasirin kan daƙile hauhawar farashi.

Da yake jawabi yayin wani taro a sakatariyar  Kungiyar Gwamnonin Nijeriya, wato Nigeria Governors’ Forum (NGF) da ke Abuja, Mataimakin Gwamnan CBN mai kula da Manufofin Tatttalin Arziki, Muhammad Abdullahi, ya bayyana cewa sauya tsarin zuwa tsarin dakushe hauhawar farashi, yana nufin komawa ga tsarin da ya fi dogaro da ƙa’idoji, gaskiya da hangen nesa, wanda ke buƙatar cikakken haɗin kai tsakanin Babban Bankin bankin Ƙasa da Gwamnatocin Jihohi.

A cewar wata sanarwa da CBN ya fitar ƙarshen makon jiya, Dakta Abdullahi ya ce duk da cewa CBN ne ke da alhakin gudanar da manufofin kuɗi domin shawo kan hauhawar farashi, matakan kashe kuɗi da manufofin kasafin kuɗi na jihohi suna taka muhimmiyar rawa wajen tasirin hauhawar farashi a ƙasa mai tsarin tarayya kamar Najeriya.

Ya bayyana cewa tsarin kashe kaifin hauhawar farashi yana da alaƙa sosai da sarrafa yadda jama’a da masu kasuwa ke sa ran tattalin arziki zai kasance. 

Yana kuma mai gargaɗin cewa rashin daidaito ko yawan kashe kuɗi ba tare da tsari ba daga gwamnatocin jihohi na iya ƙarfafa ko raunana manufofin kuɗin da CBN ke aiwatarwa.

Ya ce jihohi suna tasiri ga hauhawar farashi ta hanyoyi da dama, ciki har da:
Shawarwarin karɓar bashi, taruwar bashin cikin gida, salon kashe kuɗi, albashin ma’aikata,
gudanar da ayyukan gine-gine da ci gaba, da sauran su.

Sai kuma tsarin da gwamnatocin jihohi ke bi wajen biyan ‘yan kwangila ta hanyar bashi da kuma rashin daidaito wajen sarrafa kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayya ke rarraba wa jihohin (FAAC), da irin yanayin yadda jihohin ke biyan bashi, duk abubuwan yin la'akari da su ne.

“Ya ce a ƙasa kamar Nijeriya inda ake ta ƙoƙarin daƙile hauhawar farashi, to a gaskiya yanayin da gwamnatocin jihohi ke kashe kuɗaɗe ba bisa ƙa'ida ba, zai iya gurgunta wannan ƙoƙarin na kashe kaifin hauhawar farashi." Inji shi.

Ya buƙaci jihohi su:
Rage dogaro da cin bashin wucin-gadi,
su tabbatar da cewa bashin da suke karɓa ya dace da ƙarfin biyan bashin su. Sannan su inganta sahihancin kasafin kuɗi da kyakkyawan hasashen kuɗaɗen shiga.

Daga nan ya shawarce su cewa su riƙa fifita muhimman fannoni wajen kashe kuɗi, su riƙa daidaita tsarin kasafin kuɗi da yanayin tattalin arziki.

Abdullahi ya bayyana manyan ayyuka huɗu da suka rataya a wuyan gwamnatocin jihohi, waɗanda ya lissafa kamar haka: Kiyaye tsari da daidaito a harkokin kashe kuɗi.
Karɓar bashi cikin hikima da bin tsarin matsakaicin lokacin biyan kuɗi. Inganta haɗin kai wajen sarrafa kuɗi da bashi. Sai kuma ƙarfafa tara kuɗaɗen shiga na cikin gida.

Ya yi gargaɗin cewa kashe kuɗi ba tare da tsari ba, yawan ƙarin kasafin kuɗi da tara bashin alaƙaƙai, duk suna iya haifar da matsalar yawan kuɗi a kasuwa tare da ƙara haɗarin hauhawar farashi.

Ya ƙara da cewa shirin kashe kaifin hauhawar farashi wani yunƙuri ne na ƙasa baki ɗaya, domin samar da daidaito, amincewa da ci gaba mai ɗorewa. Duk da cewa CBN ne ke da alhakin tabbatar da daidaiton farashi, nasarar tsarin tana dogara ne kan yadda dukkan matakan gwamnati za su nuna ɗa’a a harkokin kuɗi.

Ya ce ta hanyar ƙarfafa haɗin kai da sanya daidaiton farashi a matsayin manufa ta bai ɗaya, gwamnatocin jihohi za su taimaka wajen kafa tubalin ci gaban tattalin arziki, samar da ayyukan yi da inganta walwalar jama’a.

Tun da farko, Daraktan Sashen Manufofin Kuɗi na CBN, Victor Oboh, ya bayyana tsarin a matsayin tsarin da ke amfanar iyalai, kamfanoni da gwamnatoci ta hanyar tabbatar da daidaiton hasashen hauhawar farashi, ƙarfafa amincewa da manufofin gwamnati da rage rashin tabbas a tattalin arziki.

Ya jaddada cewa ba za a iya samun daidaiton farashi ta hanyar manufofin kuɗi kaɗai ba, musamman a tsarin tarayya, yana mai cewa kashe kuɗi, karɓar bashi da yadda jihohi ke tafiyar da kuɗaɗen su suna da tasiri kai tsaye kan yawan kuɗi a kasuwa da hauhawar farashi.

A cewar sa, an shirya wannan taro ne domin ƙara fahimtar juna, bunƙasa tattaunawa da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin CBN da gwamnatocin jihohi kan rawar da kowanne ɓangare zai taka domin samun nasarar tsarin.
 

No comments