Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Lamiɗo Yuguda, Sabon Mataimakin Gwamnan CBN Ya Shiga Ofis

Sabon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Lamiɗo Yuguda, ya shiga ofis domin kama aiki a ranar Litinin, 11 ga Mayu, 2026. Yugud...

Sabon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Lamiɗo Yuguda, ya shiga ofis domin kama aiki a ranar Litinin, 11 ga Mayu, 2026.

Yuguda wanda Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa a ranar 11 Maris 2026, ya samu tarba daga manyan shugabannin CBN, ciki har da Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso.

Tun a cikin watan Afrilu ne dai Majalisar Dattawa ta amince da naɗin wanda Shugaba Tinubu ya yi wa Yuguda.

An yi wannan naɗi ne bisa ƙa'idar da Sashe na 8(1) na Dokar Babban Bankin Nijeriya ta shekarar 2007 ta gindaya.

Naɗin Yuguda ya biyo bayan naɗa tsohon Mataimakin Gwamnan CBN, Mista Bala Bello, a matsayin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tattalin Arzikin Siyasa.

Shugaban Ƙasar ya buƙace su da su gudanar da ayyukan su da ƙarin jajircewa, ƙwarewa da sadaukarwa domin tabbatar da daidaiton tattalin arzikin Nijeriya da bunƙasar sa a mabambantan matsayin da aka naɗa su.

Lamiɗo Yuguda ya taɓa riƙe muƙamin Darakta Janar na Hukumar Kula da Kasuwar Hannayen Jari ta Ƙasa (SEC), muƙamin da ya riƙe daga shekarar 2020 zuwa 2024.

Mamba ne na ƙungiyar ƙwararrun masu bin-diddigin lissafi ta ICAN.

Ya fara aikin sa a shekarar 1984 a Babban Bankin Nijeriya (CBN) a matsayin Babban Mai Kulawa a Sashen Harkokin Kuɗaɗen Waje.

Haka kuma ya yi aiki a matsayin masanin tattalin arziki a Sashen Afirka na Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), daga shekarar 1997 zuwa 2001, kafin ya koma CBN.

Ya yi ritaya daga CBN a shekarar 2016 bayan ya shafe shekaru shida a matsayin Daraktan Sashen Kula da Ajiyar Kuɗaɗe.
 

No comments