Sufeto Janar na ’Yan Sandan Ƙasa, Olatunji Rilwan Disu, ya umarci sashen sa ido na rundunar ‘yan sanda da ya gudanar da cikakken bincike kan...
Sufeto Janar na ’Yan Sandan Ƙasa, Olatunji Rilwan Disu, ya umarci sashen sa ido na rundunar ‘yan sanda da ya gudanar da cikakken bincike kan zargin da ke alaƙanta wasu manyan jami’ai biyu da lamarin bacewar tare da zargin kisan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.
Wannan umarni ya biyo bayan jerin ƙorafe-ƙorafe da aka miƙa wa ofishin IGP a ranar Juma’a daga wani lauya mai kare haƙƙin ɗan adam kuma ɗan gwagwarmaya daga Kano, Abba Hikima.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙorafen da aka gabatar sun karkata ne kan zargin da wani tsohon Mataimakin Musamman na Gwamnan Jihar Zamfara na baya, Bello Matawalle, Muhammad Musa Kamarawa, ya yi.
Kamarawa ya zargi wasu jami’an ‘yan sanda, CSP Hussaini Gimba da CSP Hassan Gimba, da cewa sun yi barazana gare shi, tare da iƙirarin cewa sun kashe Dadiyata da wasu mutane a gabansa a sansanin Operations Yaƙi da ke Kaduna.
A cikin takardun ƙorafin, lauyoyin da ke wakiltar masu ƙorafin sun bayyana cewa idan har zargin ya zama ƙarya, bincike mai gaskiya zai taimaka wajen wanke sunan jami’an da ake zargi.
Amma idan aka tabbatar da gaskiya a cikin zarge-zargen, sun ce dole ne a bi doka ba tare da la’akari da matsayi, mukami ko tasiri ba.
Haka kuma, an buƙaci a kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin gano gaskiyar abin da ya faru da Dadiyata.
Bayan karɓar ƙorafen, Babban Sufeton ‘Yan Sanda ya mika batun ga Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da Sashen Bincike da Sa Ido domin gaggauta bincike.
A cikin wasiƙar tabbatarwa, rundunar ta jaddada cewa Nigeria Police Force za ta tabbatar da bin doka da adalci a dukkan matakai.
Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, malami ne kuma mai fafutukar kare haƙƙin jama’a ta kafafen sada zumunta. An sace shi daga gidansa da ke Barnawa a Jihar Kaduna a watan Agusta 2019.
Tun daga lokacin, bacewarsa ta kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan da suka jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar, inda ƙungiyoyin farar hula da ‘yan Najeriya da dama ke ci gaba da neman a gano gaskiyar abin da ya faru da shi.

No comments