Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YOBE: Sojoji Sun Halaka ’Yan Boko Haram Sama Da 50 A Buni Gari

Sojojin Nijeriya sun kashe sama da ’yan ta’adda 50 tare da ƙwato makamai da harsasai masu yawa a yankin Buni Gari da ke Jihar Yobe. Dakarun ...



Sojojin Nijeriya sun kashe sama da ’yan ta’adda 50 tare da ƙwato makamai da harsasai masu yawa a yankin Buni Gari da ke Jihar Yobe.

Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) ne suka ragarje ’yan bindigar da suka kai hari a hedikwatar Brigade ta 27 da kuma wurin binciken ababen hawa na Buni Gari.

’Yan ta’addan sun kai harin ne da sanyin safiyar Alhamis, lokacin da ’yan ta’addan suka kai farmaki daga wurare daban-daban a cikin duhun dare.

Sanarwar da jami’in yaɗa labarai na rundunar, Laftanar-Kanar Sani Uba, ya fitar, ya ce maharan sun fara kai harin ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare ta ɓangaren yamma, kafin daga bisani su ƙara matsowa ta ɓangaren kudu kusa da Ganinga Junction, sannan suka sake kai wani farmaki ta kudu maso yamma domin mamaye sansanin sojojin.

Sai dai sanarwar ta ce dakarun sun mayar da martani da gagarumin ƙarfin wuta, lamarin da ya haddasa asara mai yawa ga ’yan ta’addan tare da tarwatsa harin da suka kai.

“’Yan ta’addan sun gamu da turjiya mai tsanani yayin da sojojin suka yi amfani da dabarun yaƙi wajen daƙile harin daga dukkan ɓangarorin,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa bayan artabun, dakarun sun ci gaba da bibiyar maharan, inda suka gano gawarwakin wasu daga cikinsu tare da makamai a cikin dazuka da hanyoyin da suka bi wajen tserewa.

Sanarwar ta ce an kuma gano alamun jini a hanyoyin tserewar, wanda ke nuna cewa da dama daga cikin maharan sun samu raunuka masu tsanani.

A cewar rundunar, ko a wani lokaci ba a samu karya garkuwar sansanin sojojin ko wurin binciken ababen hawa ba, domin an ci gaba da riƙe wuraren cikin tsaro har zuwa ƙarshen fafatawar.

Rundunar ta ce ɓangaren sojojin sama na Operation HADIN KAI ya taka muhimmiyar rawa ta hanyar gudanar da aikin leƙen asiri da sa ido, tare da kai hare-haren sama kan wuraren da aka tabbatar ’yan ta’addan sun fake yayin ja da baya.

Hukumomin sojin sun ce hare-haren saman sun kashe karin ’yan ta’adda kusan 20 yayin da jiragen yaƙi ke bibiyar waɗanda suka tsere.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogin AK-47 guda takwas, manyan bindigogi guda biyu, bama-baman RPG guda biyar, na’urorin caji na RPG guda uku, akwatunan harsasai na 7.62mm da wasu karin abubuwan fashewa.

Sojojin sun ce dakarun, tare da haɗin gwiwar jami’an sa-kai, na ci gaba da gudanar da samame domin bibiyar ’yan ta’addan da suka tsere tare da hana su sake haɗuwa.

Sai dai rundunar Operation HADIN KAI ta tabbatar da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu a yayin artabun.

Sanarwar ta yaba da jarumtar sojojin da suka rasu, tana mai cewa sun nuna kishin kasa da sadaukarwa wajen kare Nijeriya.

“Dakarunmu sun kasance a kan gaba wajen yaki da ta’addanci, inda suka jajirce domin hana ’yan ta’adda samun damar gudanar da ayyukansu a yankin Arewa maso Gabas,” in ji sanarwar.

No comments