Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MAJALISAR TARAYYA: Masu Ruwa Da Tsaki Na Ƙiru/Bebeji Sun Tsayar Da Abdulmumin Jibril Kofa Takara Karo Na Biyar

Daga Wakilin Mu Masu ruwa da tsaki na mazaɓar Kiru da Bebeji sun amince baki daya da tsayar da Abdulmumin Jibril Kofa domin sake tsayawa tak...

Daga Wakilin Mu

Masu ruwa da tsaki na mazaɓar Kiru da Bebeji sun amince baki daya da tsayar da Abdulmumin Jibril Kofa domin sake tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai karo na biyar a jere.

An cimma wannan matsaya ne bayan tuntuɓa mai zurfi da fahimtar juna tsakanin manyan shugabannin siyasa da sauran masu ruwa da tsaki a faɗin mazaɓar.

Shugaban taron masu ruwa da tsakin, Ahmad Ali Yako, ne ya sanar da hakan, yana mai cewa an yanke shawarar ce bisa la’akari da kyakkyawan tarihin wakilcin Kofa da kuma kokarinsa na bunƙasa yankin karkara.

Ya ce mazaɓar ta samu ci gaba da haɗin kai a karkashin wakilcin Kofa, yana mai cewa ci gaba da ba shi dama zai ƙara ƙarfafa nasarorin da aka samu.

Da yake bayani, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa masu ruwa da tsakin bisa cimma matsaya guda.

Ya bayyana hakan a matsayin alamar balagar siyasa da haɗin kai, tare da gode musu kan fifita muradin al’umma sama da buƙatun kai.

Gwamnan ya kuma bukaci su ci gaba da riƙe wannan haɗin kai yayin da ake tunkarar zaɓuka masu zuwa.

Ana kallon wannan matsaya a matsayin babban ƙarin ƙarfi ga matsayin siyasar Kofa yayin da ake shirin zagayowar zaɓe mai zuwa.
 

No comments