Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya Taya Murtala Garo Murnar Zama Mataimakin Gwamnan Kano

​Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Alhaji Murtala Sule Garo murnar rantsar da shi a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda Gwam...


​Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Alhaji Murtala Sule Garo murnar rantsar da shi a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, wanda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya Æ™addamar a ranar Talata.

​Gwamna Abba ya naÉ—a Murtala Garo ne domin cike gurbin da Comrade Aminu Abdulsalam ya bari, bayan murabus É—in da ya yi biyo bayan sauya sheÆ™ar gwamnan zuwa jam’iyyar APC.

​Murtala Garo, mai shekara 48, gogajen É—an siyasa ne wanda ya riÆ™e muÆ™amai daban-daban, ciki har da ​Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo,​Kwamishinan Ma’aikatar Ƙananan Hukumomi da Al’amuran Masarautu a Æ™arÆ™ashin gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, kuma É—an takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaben shekarar 2023.

​Shugaba Tinubu ya jinjina wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan naÉ—i, yana mai bayyana cewa matakin zai Æ™arfafa haÉ—in kan da ake buÆ™ata a cikin sahu da jerin mambobin jam’iyyar APC a Jihar Kano.

​Haka zalika, Shugaban ya yi kira ga É—aukacin masu ruwa da tsaki da su mara wa Gwamnan da mataimakin sa baya domin ciyar da jihar gaba. Ya kuma buÆ™aci sabon Mataimakin Gwamnan da ya yi aiki kafaÉ—a-da-kafaÉ—a da gwamna domin samar da shugabanci na gari da zai bunÆ™asa jihar.

​A karshe, Shugaba Tinubu ya yi wa Murtala Garo fatan alheri a wannan sabon nauyi da aka dora masa.
 

No comments