Jihar Kaduna ta bi sahun ƙasashen duniya wajen bikin ranar 'yancin 'Yan Jarida ta 2026, mai taken “Gina Makomar Zaman Lafiya”, inda ...
Taken na bana ya jaddada muhimmancin ‘yantacciyar kafafen yaɗa labarai masu gaskiya da ‘yanci wajen tabbatar da zaman lafiya, kare haƙƙin ɗan Adam, da kuma bunƙasa ci gaba mai ɗorewa, musamman a daidai lokacin da ake fuskantar barazanar yaɗa labarin ƙarya da lalacewar sahihancin bayanai.
A Jihar Kaduna, kafafen yaɗa labarai na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da dimokuraɗiyya, ta hanyar sanar da al’umma, tsara muhawara, da kuma ƙarfafa gaskiya da rikon amana a gwamnati.
Gwamnatin Kaduna ƙarƙashin jagorancin Sanata Uba Sani, ta ci gaba da kare ‘yancin ‘yan jarida kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, tare da samar da yanayi mai kyau da ‘yan jarida za su gudanar da aikinsu cikin ‘yanci da ƙwarewa ba tare da tsangwama ba.
A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu, Malam Ahmed Maiyaki, ya bayyana cewa:
“Goyon bayan da Gwamna Uba Sani ke bai wa ‘yancin jarida na nuna cikakken imani da cewa kafafen yaɗa labarai masu gaskiya da ƙwarewa na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya, shugabanci nagari, da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya.”
Ya ƙara da cewa, a wannan lokaci da yaɗuwar labaran ƙarya da jita-jita ke barazana ga amincewar jama’a da haɗin kan ƙasa, inda yace a rika gudanar da aikin Jarida mai dauke da bin ka'idoji da bin gaskiya domin dorewar zaman lafiya
“Jihar Kaduna za ta ci gaba da kare ‘yancin 'yan jarida tare da ƙarfafa gaskiya da rikon amana a fannin yaɗa labarai,” in ji Maiyaki.
Yayin da ƙasashen duniya ke kira da a ƙara kare ‘yan jarida da faɗar albarkacin baki, Jihar Kaduna ta sake jaddada muhimmancin kare masu aikin jarida tare da ƙarfafa bin ƙa’idoji, tantance bayanai, da kuma ƙwarewa a aikin jarida.
Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Al’adu ta Jihar Kaduna ta kuma yi alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai, tare da ƙarfafa horo da shirye-shiryen da za su taimaka wajen yaƙi da yaɗuwar ƙarya da kuma inganta sahihancin labarai.
Akan Hakan, an buƙaci dukkan masu ruwa da tsaki su rungumi gaskiya, alhaki, da mutunta juna—waɗanda su ne ginshiƙai na zaman lafiya, ilimi, da dimokuraɗiyya mai ɗorewa.

No comments