Alaƙar diplomasiyya tsakanin kasashen Nijeriya da Maroko ta ƙara nuna ƙarfafa, inda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa danganta...
Alaƙar diplomasiyya tsakanin kasashen Nijeriya da Maroko ta ƙara nuna ƙarfafa, inda ƙasashen biyu suka ƙulla yarjejeniyar ƙarfafa dangantaka a fannonin makamashi, noma, da kuma harkokin cinikayya.
Wannan sanarwa ta fito ne bayan wata tattaunawa da aka yi tsakanin Ministar Harkokin Wajen Nijeriya, Bianca Ojukwu, da takwaran ta na ƙasar Maroko, Nasser Bourita.
Babban ƙashin bayan tattaunawar shi ne aikin ginin bututun iskar gas na Nijeriya da Maroko (African Atlantic Gas Pipeline). Ministocin biyu sun bayyana wannan gagarumin aiki a matsayin "mai canza alƙiblar tattalin arziki" wanda zai samar da tsaro a fannin makamashi da kuma dunƙulewar yankin Afirka ta Yamma baki ɗaya.
Ma’aikatar Harkokin Wajen ta tabbatar da cewa tuni kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) da takwaransa na ƙasar Maroko (ONHYM) suka kammala binciken fasaha na aikin. Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Sarki Mohammed VI za su sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da aikin a rubuce kafin ƙarshen rubu'i na huɗu na wannan shekara.
Baya ga batun iskar gas, ƙasashen biyu sun tattauna hanyoyin haɗin gwiwa wajen sarrafawa da rarraba takin zamani. Wannan mataki na da nufin tabbatar da wadatar abinci ba kawai a kasashen biyu ba, har ma da sauran sassan nahiyar Afirka.
Domin farfaɗo da tsoffin yarjejeniyoyin da aka ƙulla tun zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2018, Nijeriya na shirin karbar baƙuncin taron haɗin gwiwa na ƙasashen biyu (Bilateral Joint Commission) karo na biyu.
Haka zalika, ministocin sun jaddada buƙatar sake kafa Majalisar Kasuwanci ta Nijeriya da Maroko. Sun bayyana cewa yarjejeniyar cinikayya ta bai-ɗaya ta nahiyar Afirka (AfCFTA) da kuma shirin kauce wa biyan haraji ninki biyu, za su bude sabbin kofofin bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen biyu.

No comments