Gwamnatin Kaduna Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 50 Don Ayyukan Daƙile Zaizayar ƙasa Da Ambaliyar Ruwa A Rigasa, Kawo Da Zariya Gwamnatin Jih...
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da rattaba hannu kan kwangiloli guda uku da kuɗin su ya haura naira biliyan 50 domin aiwatar da manyan ayyukan daƙile ambaliya da zaizayar ƙasa a yankunan Rigasa da Tudun Wada, Kawo da kuma cikin garin Zariya.
An gudanar da aikin ne ta hannun Hukumar Gudanar da Aikin ACReSAL ta jihar, domin magance matsalolin ambaliya da zaizayar ƙasa da ke barazana ga rayuka, kadarori da muhalli a sassan jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa bayan kammala tsarin tantance kamfanoni da bayar da kwangila cikin gaskiya, an bai wa kamfanonin Mothercat Nigeria Limited, da CGC Nigeria Limited da Spectrum Engineering Limited damar gudanar da ayyukan.
Aikin yankin Rigasa da Tudun Wada wanda kamfanin Mothercat Nigeria Limited zai gudanar ya kai sama da kilomita 17, inda za a gina manyan magudanan ruwa na siminti tare da aiwatar da ayyukan da za su taimaka wajen daƙile zaizayar ƙasa da kuma tafiyar da ruwa yadda ya kamata.
Hakazalika, aikin yankin Kawo wanda aka bai wa Spectrum Engineering Limited zai mamaye sama da kilomita uku, inda za a faɗaɗa hanyoyin ruwa tare da amfani da duwatsu da wasu hanyoyin kare ƙasa daga lalacewa.
Shi kuwa aikin yankin Zariya wanda kamfanin CGC Nigeria Limited zai aiwatar zai zarce kilomita 11, tare da gina hanyoyin kariya domin kare al’umma da kadarori daga illar ambaliya da zaizayar kasa.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ayyukan wani bangare ne na ƙoƙarin ta wajen kare muhalli, magance sauyin yanayi da kuma tabbatar da dorewar ci gaba a fadin jihar.
Ta ƙara da cewa ana sa ran ayyukan za su taimaka wajen kare rayuka da dukiyoyi, bunƙasa harkokin tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al’ummomin da abin ya shafa.
Haka kuma gwamnatin ta jaddada ƙudurin ta na ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi jin dadin jama’a da kare muhalli a dukkan sassan jihar.

No comments