Rundunar Tsaro ta Kasa (DHQ) ta kare harin sararin samaniya da dakarun soji suka kai a Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja, inda ta ce ...
Sanarwar, wadda Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar, ta ce an kai harin ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu kan taruwar miyagun a ƙauyen Lukupe ranar 9 ga watan Mayun 2026.
Rundunar ta bayyana cewa dakarun sojin ƙasa masu sarrafa jiragen yaƙi marasa matuƙi (UAV) ne suka ƙaddamar da harin tsakanin ƙarfe 11:59 na daren Asabar zuwa karfe 6:00 na safiyar Lahadi, 10 ga watan Mayu. Wuraren da harin ya shafa sun haɗa da ƙauyukan Katerma, Bokko, Kusasu da Kuduru
Sojoji sun bayyana cewa a ƙauyen Kusasu kaɗai, an yi nasarar hallaka aƙalla ’yan bindiga 70, yayin da sauran suka tsere a kan babura zuwa yankin Zango.
Duk da koke-koken da wasu mazauna yankin ke yi na cewa bama-baman sun faɗa gidajen su, musamman a unguwar Guradnayi, rundunar tsaron ta ce bayanan da take da su ba su nuna hakan ba.
Rundunar ta ce galibin mazauna waɗannan ƙauyuka tuni suka ƙaurace wa gidajensu zuwa garin Sarkin Pawa saboda gudun hare-haren ’yan bindiga, don haka wuraren da aka kai harin sansanonin bata-gari ne kawai.
"Rundunar soji za ta ci gaba da aiki don kakkabe sansanonin ’yan bindiga da nufin dawo da zaman lafiya a yankin Shiroro da sauran sassan jihar." — Maj. Gen. Onoja
A ƙarshe, rundunar ta yi kira ga jama'a da kafafen yaɗa labarai da su guji yaɗa labaran da ba a tantance ba, waɗanda za su iya jefa mutane cikin fargaba ko kuma su kawo cikas ga ayyukan tsaro da ake gudanarwa.

No comments