Daga Zubairu Lawal, Lafia Jam'iyyar Adawa ta PDP ta fara tantance 'yan Takarar Zaben fidda gwani na shekarar 2027 a jihar nasarawa....
Jam'iyyar Adawa ta PDP ta fara tantance 'yan Takarar Zaben fidda gwani na shekarar 2027 a jihar nasarawa.
A ranar Laraba 13/5/2026 ne 'ya'yan Jam'iyyar suka yi dafifi a harabar Jam'iyyar da ke kan titin Jos cikin garin Lafia tare da murnar yabon 'yan takarar su.
'Yan Takarar kujerun Majalisan Dattijai dana Majalisan wakilai dn na Majalisan dokoki Jihar Sun samu halartar wajen tantance war.
Da yake zantawa da manema Labarai, Shugaban tawagar Masu tantance 'yan takarar, Hon. Salami S. Baba ya ce; Suna samun haɗin kan 'yan takarar a lokacin aiki.
Ya ce; duk 'yan yakarar kawo ya samu maki Mai yawa wajen tantancewar. Babu tangarɗa .
Shi ma a nasa jawabin Shugaban Jam'iyyar PDP ta ƙasa reshen Jihar Nasarawa Hon. Daniyel Gimba ya ce; Jam'iyyar PDP na da ƙwarin giwar lashe zabe a Jihar Nasarawa.
Ya ce; duk Waɗanda suka saya from na takara mutane ne masu jama'a. Kowa na da ƙwarin gwiwar a mazaben sa.
Ya ce; siyasan bana, Jam'iyyar PDP za ta taka rawa fiye da zabukan baya.
Ya yi kira ga al'umman Nijeria da su ƙaurace wa Jam'iyyar APC da ta jefa al'ummar ƙasa cikin ƙuncin rayuwa.
Ya ce; al'umman Nijeriya ba su taba ganin baƙin mulki Irin wannan ba.
Su ma 'yan takarar sun nuna ƙwarin gwiwar Nasar a zabukan 2027. A lokacin da suke tattaunawa da manema Labarai bayan tantance su.

No comments