Sauye-sauyen da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya aiwatar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Olayemi Cardoso, sun taimaka matuka wajen dawo da sha’aw...
Haka kuma yin amanna dangane da yadda ake tsara shirye-shiryen manufofin kuɗi bisa gaskiya, da kuma tabbatar da daidaito a kasuwar musayar kuɗaɗen waje, su ma sun taka muhimmiyar rawa wajen antayo wasu zuba jari cikin Nijeriya daga waje.
Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen shi ne sassautawa da kuma haɗe tsarin musayar kuɗaɗen waje zuwa kasuwar musayar kuɗi ta bai-ɗaya. Kafin waɗannan gyare-gyare, yawaitar farashin musayar kuɗaɗe daban-daban da kuma ƙarancin dala sun hana masu zuba jari daga ƙasashen waje shiga kasuwannin zuba jari a Nijeriya, saboda tsoron rashin samun damar mayar da ribar su zuwa ƙasashen su.
Matakin da CBN ya ɗauka na komawa tsarin da kasuwa ke ƙayyade farashin musayar kuɗaɗe, tare da ƙoƙarin kawar da giɓin buƙatar kuɗaɗen waje, ya rage rashin tabbas tare da inganta yawan kudaden da ke zagayawa a matsayin kuɗaɗen hadahada a kasuwar musayar kuɗaɗe.
Waɗannan sauye-sauye sun kuma ƙarfafa amincin tattalin arzikin Nijeriya.
Sai kuma tsauraran manufofin hadahadar kuɗi da ƙarin kutdin ruwa sun sanya takardun baitulmalin gwamnati da takardun bashi na Nojeriya suka zama masu jan hankali ga masu zuba jari daga ƙasashen waje da ke neman riba mai yawa a kasuwannin ƙasashe masu tasowa.
Masana tattalin arziki sun bayyana cewa masu zuba jari sun ƙara nuna sha’awar dawowa Nijeriya saboda kasuwar kuɗaɗen waje ta fi samun tsari da kuma tabbaci a yanzu.
Yayin da ƙwarin gwiwa ya karu, kuɗaɗen da ke shigowa cikin Nijeriya daga waje sun ƙaru sosai.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa kuɗaɗen da suka shigo Nijeriya sun ƙari da kusan kashi 90 cikin 100 a shekarar 2025, inda suka kai dala biliyan 23.22, wanda akasari ya fito daga masu zuba jari na ƙasashen waje da suka saka kuɗaɗe a takardun bashi.
Kayan kasuwar kuɗi da kuma hannayen jari:
Ɓangaren bankuna ya kasance ɗaya daga cikin manyan waɗanda suka amfana da dawowar ƙwarin gwiwar masu zuba jari. Rahotanni sun nuna cewa bankunan Nijeriya sun tara kusan naira tiriliyan 4.61 a ƙarƙashin shirin ƙarfafa jariin bankuna, inda kusan kashi 27 cikin 100 ya fito daga masu zuba jari na ƙasashen waje.
Sannan kuma shiga kasuwar hadahadar hannayen jarin Nojeriya daga ƙasashen waje ta farfaɗo sosai.
Bayanai daga 'Nigerian Exchange Group' sun nuna cewa masu zuba jari daga ƙasashen waje sun sayi hannayen jarin Nijeriya da suka haura naira tiriliyan 1 cikin watanni tara na farkon shekarar 2025, wanda ya nuna babban ƙarin shiga idan aka kwatanta da shekarun baya.
Wani babban abu da ya ƙara ƙwarin gwiwar masu zuba jari shi ne ƙaruwar ajiyar kuɗaɗen ƙetare na Nijeriya.
CBN ya bayyana cewa ajiyar kuɗaɗen waje ta kai kusan dala biliyan 45.5 zuwa kartshen shekarar 2025, abin da ya taimaka wajen daidaita darajar naira tare da tabbatar wa masu zuba jari cewa ƙasar na da ikon cika alƙawurran ta na ƙasashen waje.
Masana harkokin kuɗi da hukumomin tantance matsayin tattalin arziki sun kuma yi maraba da waɗannan gyare-gyare. Kamar kuma yadda rahotanni suka nuna cewa haɗarin kasadar zuba jari a Nijeriya ya ragu yayin da sauye-sauyen suka dawo da ƙwarin gwiwar masu zuba jari.
Za a iya fahimtar cewa sauye-sauyen CBN sun taimaka wajen sauya yadda masu zuba jari ke kallon Nijeriya daga kasuwar da ake ganin tana da haɗari da kasadar rashin tabbas a manufofi zuwa ƙasa mai ƙoƙarin dawo da amincewa ta hanyar gyare-gyaren da suka dace da tsarin kasuwa, ingantaccen tsarin kulawa, ƙarin tsare-tsare na gaskiya a harkar kuɗaɗen waje, da kuma tsauraran manufofin hadahadar kuɗi.
Duk da cewa har yanzu akwai ƙalubale kamar hauhawar farashi, biyan basussuka da matsalolin rashin ingantattun ababen more rayuwa, masu zuba jari da dama yanzu suna ganin kadarorin Nijeriya sun fi jan hankali da sauƙin shiga fiye da yadda suke a baya.

No comments