Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnati Za Ta Jibge Jami'an Tsaro A Nasarawa Yayin Zaben Fidda Gwani Na APC -Kwamared Piter

Daga Zubairu M. Lawal Lafia  Gwamnatin Jihar Nasarawa ta tanadar da isasun jami'an domin gudanar da Zaben fidda gwani na Jam'iyyar A...

Daga Zubairu M. Lawal Lafia 

Gwamnatin Jihar Nasarawa ta tanadar da isasun jami'an domin gudanar da Zaben fidda gwani na Jam'iyyar APC da zai fara daga ranar Juma'a 15/ 5/2026.

Da yake zantawa da manema Labarai Mai taimaka wa Gwamna Abdullah sule Bangaren mu'amala da al'ummar Jihar, Kwamared Piter Ahmba ya bayyana cewa, Gwamnati ta ɗauki wannan mataki ne domin gudanar da sahihin Zabe cikin kwanciya hankali.

Kwamared Piter Ahmba ya ce; babu wani ɗan takarar da Gwamnatin Jihar ta tilasta masa ya janye wa wani.

Yace duk cikan su sun cancanta Kuma kowa zai taka mahimmiyar rawa idan aka tsayar da shi Takara.

Za a Kuma  gudanar da Zaben Kai tsaye ba tare da magun-magun ba. Za a gudanar da Zaben gaskiya da gaskiya kamar yadda dokan Zabe ya tanada.

Za a yi amfani da sahihin Katin Jam'iyyar Wanda yake da cikakken sheda.

 Kwamared ya yaba wa 'yan takarar Jam'iyyar APC da suke gudanar da harkokin Siyasa cikin tsafta da ƙaunar juna a Jihar.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar ta sha alwashin bayyana duk ɗan takarar da ya yi nasara.

Daga ƙarshe ya yi kira ga 'yan jaridu da su kasance masu bayyana sahihin labarin da ya gudana a Zabe ba tare da nuna wariya ba.

Ya ce al'umman Jihar da ba su samu damar zuwa wajen ba, za su dogarane da kafafen yaɗa labarai. A don haka ya kamata a ji gaskiya daga garesu.

 

No comments