Daga Zubairu Lawal, Lafia Jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ta amince da tsohon muƙaddashin Akanta Janar na Tarayya, Alhaji Abubakar Giz...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP) ta amince da tsohon muƙaddashin Akanta Janar na Tarayya, Alhaji Abubakar Giza, a matsayin don takararta na bai-ɗaya domin tsayawa takarar gwamnan jihar Nasarawa a zaben gwamnoni mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Mista Cletus Ogah, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke Lafia, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne saboda ƙwarewar shugabanci da kuma taimakon da Abubakar Giza ke bai wa marasa galihu a jihar.
A cewar Mista Cletus Ogah, “Takara tasa za ta sauya abubuwa da dama a jihar Nasarawa. Kuma kamar yadda na fada tun farko, har yanzu ana sayar da fom ɗin mu.
"Muna da tausayi da la’akari da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki yanzu. Mata na shan wahala sosai, saboda haka kudin fom dinsu kyauta ne.
“Haka kuma matasa za su ci gajiyar wannan damar, domin daga shekaru 25 zuwa 29 za mu ba su fom kyauta, ko suna neman takarar Sanata ne, ko Majalisar Wakilai ko kuma Majalisar Dokokin Jiha,” in ji shi.
Tun da farko, yayin bayyana aniyarsa ta tsayawa takara, Alhaji Abubakar Giza ya ce shigarsa takarar gwamna ba wai saboda kiraye-kirayen da ake masa ba ne kaɗai, har ma da irin ayyukan da ya taba yi da kuma ƙarfin sa na kawo ƙarin ci gaba a jihar.
A cewar Abubakar Giza, “Matakina ya samo asali ne daga damuwar da nake da ita kan halin da jama’a ke ciki.
Matasa na neman dama amma suna samun kofar a rufe. Ma’aikatan gwamnati na buƙatar mutunci a aikinsu, haka kuma masu ritaya da fansho suna bukatar a biya su haƙƙoƙin su da kuɗaɗen fansho gaba ɗaya.
“Haka kuma al’ummomin karkara na buƙatar hanyoyi na zamani. Sama da komai kuma akwai buƙatar samar da tsaro da zaman lafiya mai ɗorewa.”
Ya ƙara da cewa hangen nesansa mai sauki ne amma mai karfi, wato samar da jihar Nasarawa mai inganci, tsaro da kuma kula da muradun jama’a.
“Idan aka ba ni dama, gwamnatina za ta mayar da hankali wajen farfado da tattalin arziki da samar da ayyukan yi.
“Zan bunƙasa sarkar darajar noma, inganta ƙanana da matsakaitan sana’o’i, tare da jawo hannun jari da zai samar wa al’ummar jihar Nasarawa ayyukan yi na gaskiya,” in ji shi.

No comments